Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ba da shawara ga jihohin Arewacin Najeriya masu fama da matsalar rashin tsaro. Ya bukaci su yi koyi da tsarin da ya kawo.
Rahotanni sun nuna cewa mambobin majalisar dokokin jihar Legas sun sauke shugaban majalisar, Rt. Hon. Mudashiru Obasa daga mukaminsa yau Litinin.
Sanata Samuel Anyanwu ya koma bakin aiki a matsayin sakataren jam'iyyar PDP na kasa. Anyanwu ya ce ya daukaka kara kan hukuncin kotu da ya sauke shi.
Tsagerun 'yan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a jihar Borno. 'Yan ta'addan sun hallaka mutane tare da kona gidaje masu yawa a harin da suka kai.
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta tabbatar da rasa rayukan fararen hula a harin da sojoji suka kai kan ƴan ta'adda.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa a yanzu ya sauya ra'ayi kan adawar da yake yi dangane da kudirin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya sauke kwamishinan yaɗa labarai daga muƙaminsa, an ce hakan ba zai rasa nasaba da rashin aikin da ya kamata ba.
Kamfanin rarraba wutar lantarki watau TCN ya ce babu abin da ya ssmu babban layin wuta, layin Benin-Omotosho kawai ya ɗan samu matsala kuma ana kan gyara.
An shiga jimami a kasar India bayan wani dan majalisar dokoki ya bindige kansa. Dan majalisar mai suna Gurpreet Gopi ya rasu ne bayan ya harbi kansa bisa kuskure.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari