Manyan Labarai A Yau
Rahotanni sun nuna cewa yan ta'adda da ake tunanin mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki fadar shugaban kasar Chadi amma sun gamu da fushin dakarun sojoji.
Jami'an tsaron hadin gwiwa da suka hada da 'yan sanda da na rundunar tsaron Sokoto sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan bindiga suka kai kan matafiya.
Gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin sadarwa su yi ƙarin kudin kiran waya, sako da sayen data amma ba zai kai kaso 100% ba in ji ministan sadarwa, Bosun Tijani.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi martani ga jam'iyyar APC kan shirinta na ganin mulkin Kano ya dawo hannunta a zaben 2027. Ya ce Allah ke ba da mulki.
Kwamoshinan harkokin yawon bude ido, al'adu da fasaha na jihar Kuros Roba, Abubakar Robert Ewa ya mutu a asibitin Kalaba jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta ɗauki matakin ladabtarwa kan jami'anta da ake zargi da aikata sata.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika da sakon gargadi ga 'yan majalisar zartarwar jihar. Gwamna Abba ya ce ba zai lamunci rashin biyayya ba.
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum ya ja kunnen masu amfani da kafafen sada zumunta kan yada labaran karya a kan PDP.
Wani jami'in rundunar tsaron jihar Sokoto ya riga mu gidan gaskiya bayan ya harbi kansa bisa kuskure. Lamarin ya faru ne bayan an ceto wasu mutanen da aka sace.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari