Manyan Labarai A Yau
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai kan harin da 'yan bindiga suka kai a Kebbi. Ya ba gwamnatin Tinubu shawara.
An tabbatar da mutuwar fitaccen dan jarida kuma daya daga cikin wadanda suka kafa mujallar Newswatch, Dan Agbese, ya mutu yana da shekaru 81 da haihuwa.
Karamin ministan tsaro, Dr Bello Matawalle, ya nuna alhininsa kan sace dalibai mata da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi. Ya ce an ba jami'an tsaro umarnin ceto su.
A wata na bakwai a jere, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta sauka zuwa 16.05% a watan Oktoba, 2025 idan aka kwatanta da watan Satumban da ya gabata.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi gargadi kan yawan sauya shekar da wasu 'yan siyasa suke yi zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Babban lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya bada shawara ga mutanen da 'yan bindiga suka sace kan matakin da za su dauka.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya fito ya musanta rahotannin da ke cewa ya samu sabani tsakaninsa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF), ya bayyana cewa za su iya kawo karshen 'yan bindiga cikin shekara daya idan gwamnati ta yi abin da ya dace.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya koka kan kashe-kashe a Najeriya. Ya bayyana cewa yana shiga mawuyacin duk lokacin da ya samu labarin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari