Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriy masu aikin samar da tsaro sun yi nasarar shirya harin kwanton bauna kan 'yan ta'addan ISWAP. Sun kwato makamai a hannun miyagun.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Neja inda suka tafka ta'asa. Miyagun sun hallaka 'yan sa-kai tare da yin awon gaba da mutane da dama.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya musanta batun cewa ya janye karar da ya shigar da jam'iyyarsa ta PDP a gaban kotu. Ya ce ba gaskiya bane.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi karin haske kan dalilinsa na shigar da jam'iyyar PDP kara a gaban kotu. Ya ce yana son kwatar hakkinsa ne.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin gabatar da kasafin kudin 2026, wanda zai kafa tarihin zama na farko da zai lakume akalla Naira tiriliyan 1 a jihohin Arewa.
Tsohon kwamishinan yada labarai, Don Adinuba ya ce labarin da ke yawo cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya mutu a birnin Landan na Birtaniya.
Yan majalisa 12 a Ondo sun fara shirin tsige kakakin majalisar jihar, Olamide Oladiji bisa zargin rashawa, karkatar da N50m da sabawa kundin tsarin mulki.
'Yan majalisar wakilai na jam'iyyar NNPP sun fito sun yi bayani kan jita-jitar da ke cewa suna shirin sauya sheka daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyu.
An samu hatsaniya tsakanin dakarun sojojin Najeriya da jami'an 'yan sanda a jihar Benue. Fadan wanda ya auku sakamakon sabani ya jawo an jikkata mutum daya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari