Manyan Labarai A Yau
Hadimin Peter Obi kuma shugaban kungiyar Obidients Movement, Yunusa Tanko, ya bayyana cewa babu wani shirin hadewa tsakanin ubangidansa da Goodluck Jonathan.
Hukumar NEMA ta ce mutum 236 sun mutu a ambaliyar ruwa da ta shafi jihohi 27 da Abuja, yayin da fiye da 400,000 suka rasa gidaje da gonaki a fadin kasa.
Tsohon ministan sufuri a gwamnatin marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mu'azu Sambo Jaji, ya tabo batun ficewa daga jam'iyyar APC. Ya ce zama daram.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya gwangwaje wata Hajiya da kyautar kudade. Gwamna Mutfwang ya ba ta kyautar ne kan mayar da kudaden da ta tsinta a Saudiyya.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Nasarawa. 'Yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya. Daniel Bwala ya nuna yatsa ga kasashen Yamma.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya nuna damuwarsa kan sauya shekar da wasu ke yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Ya ce ya damu matuka sosai.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da yi wa mutane 175 afuwa cikinsu har da wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, Maryam Sanda za ta koma cikin iyalanta.
Jami'an Tsaron filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas sun cafke wasu matasa dauke da kudi tsaba, sama da Dalar Amurka biliyan 6.1.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari