Jihar Legas
NDLEA ta kai samame a otal din Emerald dake unguwar Ladipo a jihar Legas inda aka kama wasu alhazan Najeriya suna kokarin hadiye hodar iblis gabanin tashinsu.
Hukumomi a Jami'ar jihar Lagos sun yi martani bayan samun satifiket na digiri a hannun masu siyar da nama a jihar inda suka ce an dade da daukar mataki kan lamarin.
Rahotanni sun bayyana an kwashi 'yan kallo a wani bankin Polaris da ke jihar Legas bayan da kungiyar kwadago ta NLC ta dura bankin tare da fatattakar jama'a.
An shiga takaici a jihar Lagos bayan zuciyar wata ‘yar kasuwa, Alhaja Iyabo ya buga, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta saboda rushe shagonta da N50m a ciki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta samu nasarar damke wata mata mai shekaru 21 da jaririn da ta sato wanda tuni ta shaidawa mutane cewa ita ce ta haihu.
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Legas ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazan jihar, Idris Oloshogbo, wanda ya rasu bayan dawowa daga Ɗawafi a Makkah.
Aliko Dangote ya sanar da cewa zuwa karshen shekarar 2025 duka motocinsu da ke kamfanin siminti za su koma amfani da gas domin rage dogaro da fetur.
Wata uwa da danta sun gamu da fushin hukumar bayan gurfanar da su gabanta da zargin satar kayan kamfani da suka tasamma miliyoyin naira a jihar Lagos.
Jami'an hukumar hana fasakwauri ta bayyana dakile yunkurin shigo da buhunhunan shinkafa 'yar waje akalla 6,467 ta iyakar Seme wanda ya kai tirela 10.
Jihar Legas
Samu kari