Kasuwa Ta Buɗewa Fasto Mai Saida Sabulu, Turare, Riga da Masoron 'Mu'ujiza'

Kasuwa Ta Buɗewa Fasto Mai Saida Sabulu, Turare, Riga da Masoron 'Mu'ujiza'

  • Wani babban malamin addinin Kirista, Jeremiah Fufeyin ya baje-kolin sayar da kayayyakin mu'ujiza domin taimakon Jama'a
  • Fasto Jeremiah Fufeyin mai shekaru 52 ya baza komarsa ta kasuwanci yana sayar da sabulu, turare, riga da kuma wani masoro
  • Limamin cocin ya buƙaci jama'a da su siya domin samun arziki na duniya tare da samun kariya daga dukkan matsaloli da cutuka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jeremiah Fufeyin, faston da ya assasa cocin CMDM, ya janyo cece-kuce a soshiyal sada zumunta bayan da ya ƙaddamar da wani sabon salon kasuwanci tare da ci da addini.

Soshiyal midiya dai ta rikice da bidiyon Fasto Fufeyin yana nuna sabulu, turare, riga da masoro da ya yi ikirarin na mu'ujiza ne.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike: Ministan Tinubu ya gigita 'yan Najeriya da rigar kusan Naira miliyan 3

Fasto ya gabatar da kayayyakin mu'ujiza ga mabiyansa
Shugaban cocin CMDM ya gabatarwa mabiyansa turare, riga da subulun mu'ujiza. Hoto: Prophet Jeremiah Omoto Fufeyin
Asali: Facebook

A wani bidiyon zaman addu'a na kai tsaye da aka wallafa a shafin Facebook, an ga Fasto Fufeyin da matarsa, Anthonia, sun kaddamar da kayayyakin da suka ce na mu'ujiza ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto ya gabatar da sabulun mu'ujiza

Faston ya ce sabulun yana da ƙarfi kuma zai iya magance kowacce cuta, inda yace sabulun zai taimakawa mutanen da ke da rashin sa'a ko samun tsaiko a cimma burikansu a rayuwa.

Premium Times ta ruwaito Fasto Fufeyin ya bayyana cewa wasu mutane na fama yayin da wasu ke halartar cocinsa ba tare da sanin koyarwa Ubangiji ba.

Fasto ya yi bayanin turaren mu'ujiza

Yayin wa'azin na kai-tsaye, Fasto Fufeyin ya yi ikirarin cewa turaren da ya sarrafashi yana karya duk wani shingen rashin nasara ta dan Adam.

"Akwai wasu mutane wadanda duk abin da za su yi basa samun ci gaba, hatta kudin da ke asusun bankinsu ba sa karuwa sai dai su ragu.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane sun mutu yayin da ginin katafaren Otal ya rufta a Abuja

"Irin waɗannan mutanen na buƙatar amfani da irin wannan turare. Wannan turaren yana ba da gudumawa wurin samun nasara.

- Fasto Jeremiah Fufeyin

Bayanin masoro da rigar mu'ujizar Fasto

Kamar yadda malamin addinin ya bayyana, masoron da ya sarrafa na iya sa a tsallake duk wata matsalar da wanda ya sayi fili amma ya kasa ginawa yake fuskanta.

Hakazalika ya bayyana wata riga da yayi iƙirarin cewa tana bada kariya sannan tana kawo albarka.

Kalli bidiyon a kasa:

Wike ya rikita jama'a da rigar N3m

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya rikita 'yan Najeriya da salon gayunsa a Abuja.

An ga wani bidiyo wanda ya nuna Wike ya saka rigar kusan Naira miliyan uku inda ya halarci wani taro, lamarin da ya haifar da surutu a soshiyal midiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.