"Kara Tsufa Nake Yi”: Jarumar Fim Ta Koka Kan Rashin Miji, Ta Jero Dalilai

"Kara Tsufa Nake Yi”: Jarumar Fim Ta Koka Kan Rashin Miji, Ta Jero Dalilai

  • Yayin da aka kammala auren mawaki Davido, jarumar fim a Nollywood ta sha jinin jikinta inda ta kwadaitu da aure
  • Jaruma Nkechi Blessing ta koka kan yadda take kara tsufa amma babu mijin aure inda ta ce ta shirya tuntuni
  • Ta ce soyayya akwai dadi kada ka kuskura wani ya fada maka sabanin haka inda ta ce a yanzu ta shirya yin aure ita ma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Jarumar fim a masana'antar Nollywood, Nkesci Blessing ta nuna damuwa kan yadda take zaune babu aure.

Blessing ta ce ta gaji da zama babu aure kuma ga shi kullum kara tsufa take yi inda ta roki ubangiji ya kawo mijin aure.

Kara karanta wannan

"NNPP ta barar da damarta": APC ta fadi yadda za ta kwace mulkin Kano da Zamfara

Jarumar fim ta shiga damuwa kan rashin mjin aure
Jarumar fim, Nkechi Blessing ta ce ta shirya aure amma babu mijin aure har yanzu. Hoto: @nkechiblessingsunday.
Asali: Instagram

Nkechi: Jaruma ta damu kan rashin aure

Jarumar ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram a inda ta bayyana auren mawaki Davido ya sake daga mata hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta nuna kwadaituwa ga yin aure tun bayan na Davido da Chioma inda ta bukaci taya ta neman sunan da za ta hada da na saurayinta.

Har ila yau, ta bayyana cewa tana shan matsi daga mutane kan maganar aure inda ta ke tsoro yadda kullum tsufa kan cin mata.

Nkechi ta fadi abin da yaja hankalinta

"A ranar 25 an yi na 'Chivido' na ji wani iri a auren, nima ina ta tunanin aurena yadda zan hada suna na da saurayina."
"Na shirya, a baya ne ban shirya ba, za su yi ta damunka a kan aure kuma wai ace kada ka tsorata, ina tsoro gaskiya."

Kara karanta wannan

"Akwai wahala": Matar tsohon shugaban kasa ta ce ko kyauta ba za ta koma 'Aso Rock' ba

"Yawan matsin lamba ya yi yawa, kada ka yarda wani ya fada maka sabanin haka, soyayya da dadi, ka duba yadda suke murmushi."

- Nkechi Blessing

Jarumar fim ta soki Kiristoci kan Davido

A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa jarumar fim a Nollywood, Merit Gold Eberechi ta caccaki Kiristoci kan taya Davido murnan aurensa.

Jarumar ta ce hakan munafurci ne tun da kowa ya sani sun haifi 'ya'ya uku ba hanyar aure ba wanda idan wasu ne sai a yi ta sukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.