Lafiya Uwar Jiki
Kasancewar Shinkafa ta zamto gama-gari a fadin duniya, domin kuwa abu ne mai wuya a rasata a gidan Talaka da mai kudi sakamakon yadda al'ummar duniya suka kafa mata kahon zuka na ta'ammali da ita kusan kowace rana zata hudo kai.
Kasancewar barasa akwai dadin dandano a baka da kuma harshe, hakan bai sanya ta tsarkaka da illata masu ta'ammalli da ita ba, ta yadda a wani sa'ilin take rugu-rugu da dukkan wata garkuwa ta lafiya da jikin dan Adam yake da ita.
Shugaban hukumar lafiya na duniya, Jonathan Quick, yace cutar na iya kama kimanin mutum miliyan 33, don zata yadu ne a duniya ta hanyar dabbobi zuwa ga mutane, wadda za’a iya ganewa bayan shigarta jikin mutum da kwanaki hudu...
Dan itacen Dabino baya da iyaka ta fuskar alfanu da kuma shahara a kasashen Larabawa, wanda ya samo asali tun a farkon duniya da ya kasance daya daga cikin nau'ikan abinci na Annabawa da mutanen da suka shude shekaru aru-aru.
Shi dai Kimchi wani nau'in abinci ne da ya fi shahara a al'adar mutanen kasar Koriya, wanda ake hada shi ta hanyar turara ganyeyyaki irin su Kabeji tare da kayan hadi domin kari dandano da suka shafi gishiri, tafarnuwa da citta.
Kamar yadda gama garin al'umma su ka san amfanin gishiri a matsayin mai kara dandado ga abincin mu na yau da gobe, ana kuma amfani da shi wajen bangaren kiwon lafiya sakamakon muhimman sunadari da sirrika da ya kunsa.
A ranar Talata 6 ga watan Maris da ta gabata ne, gwamnatin jihar Buachi ta bayar da rahoton salwantar rayukan mutane uku, bayan da bincike ya tabbatar da mutane 25 masu dauke da cutar Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar.
Da yawan mutane sukan ribaci alfanun dake kushe cikin tafarnuwa wajen kiwatar lafiyar su. Akan yi amfani da ruwan tafarnuwa wajen kawar da cututtukan da suka shafi kirji inda take da matukar tasiri wajen kawar da cututtukan hunhu.
A yayin da cutar hawan jini ke neman zama ruwan dare mai gama duniya, akwai nau'ikan cututtuka biyar da kuma take haifarwa. Jaridar NAIJ.com ta kawo muku nau'ikan cututtuka biyar da hawan jini ke haifar wa kamar haka.
Lafiya Uwar Jiki
Samu kari