Lafiya Jari: Amfani 10 na Dabino ga lafiyar bil Adama

Lafiya Jari: Amfani 10 na Dabino ga lafiyar bil Adama

Dan itacen Dabino baya da iyaka ta fuskar alfanu da kuma shahara a kasashen Larabawa, wanda ya samo asali tun a farkon duniya da ya kasance daya daga cikin nau'ikan abinci na Annabawa da mutanen da suka shude shekaru aru-aru da suka gabata.

A sakamakon shaharar Dabino a kasashen larabawa, ya sanya wadansu da suka juya baya ga addinin Islama na masa kallon abincin musulmai ne kadai.

Dabino

Dabino

Wasu kwararrun masana kiwon lafiya sun yi hasashen cewa, babu wata illa da dan Dabino ke da ita ga lafiyar dan Adam, wanda ya kunshi sunadarai da suka hadar da; Vitamins, Minerals, Oil, Fiber, Calcium, Sulfur, Iron, Potassium, Phosphorus, Manganese, Magnesium, da kuma Copper.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa a garin Kaduna

Da sanadin taka rawar gani na wannan sunadarai, Legit.ng ta kawo muku sirrika goma da Dabino ya kunsa kamar haka:

1. Inganta lafiya da karfin kassan jiki.

2. Warware matsalolin hanji.

3. Inganta lafiyar kwakwalwa.

4. Habaka lafiyar zuciya.

5. Inganta lafiyar ma'aurata.

6. Kariya ga cutar Daji.

7. Waraka daga cutar amai da gudawa.

8. Kariya daga cutar shan inna.

9. Inganta garkuwa jiki.

10. Sanya kuzari da karfin jiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel