Bincike: Yawan Baccin rana yana da nasaba da cutar Alzheimer's
A wani sabon bincike da aka wallafa a mujallar JAMA Neurology, masana ilimin kimiya sun bayyana cewa, yawaitar baccin rana alama ce da take nuna cewa dattijai na fama da cutar Alzheimer's mai kone duk wani tunani na kwakwalwar dan Adam.
A cewar masana, yawan bukatuwa ga baccin rana yana da dangantaka mai karfi ga taruwar kwayoyin cuta na beta-amyloid a cikin kwakwalwa.
Wannan kwayoyin cuta sukan addabi duk wata kwayar halitta dake cikin kwakwalwa wajen dakile tashoshin sadarwa a tsakanin su.
KARANTA KUMA: Gwamnatin APC ta yiwa ta PDP fintinkau ta fuskar rashawa - Secondus
Legit.ng ta fahimci cewa, kwararrun masana sun gudanar da wannan bincike ne a asibitin Mayo Clinic dake kasar Amurka, inda aka samu maza kaso 72.1 da kuma mata kaso 27.0 cikin 100 dauke da kwayoyin cutar.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a yau Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Yobe inda zai gana da iyayen 'yan Matan Dapchi da aka sace tun a watan da ya gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng