Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci dake haddasa ciwon Koda

Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci dake haddasa ciwon Koda

Wani kwararren likitan Koda, Long John Adonye, ya bayyana cewa yawan ta'ammali da magunguna daban-daban, gishiri da sunadarai a abinci su kan haddasa ciwon koda ga dukkan jinsi na mata da maza kamar yadda bincike ya tabbatar.

Adonye wanda kwararren likita ne a asibitin koyarwa na jami'ar Legas ta Idi-Araba ya bayar da wannan shawara ne a yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa, a yayin tunawa da ranar Koda ta duniya ta ranar 8 ga watan Maris na kowace shekara.

Yake cewa, mafi akasarin magunguna da mutane ke amfani da su ba tare da likita ya rubuto ma su ba ya kan haddasa cututtukan sakamakon amfani da su ta hanyoyi da ba su dace ba.

Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci dake haddasa ciwon Koda
Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci dake haddasa ciwon Koda

A cewar sa, ciwon Koda matsala ce mai girman gaske ga dukkan jinsi, kazaliza akwai matukar wuya wajen kulawa da ciwon wanda a yanzu itace cuta ta takwas a duniya mafi haddasa mutuwar mata.

Wannan shine babban kalubale da ya sanya masana kiwon lafiya ke shawartar al'umma wajen kiyaye cimar su da kuma kulawa da lafiyar jikin su wajen motsi, shan ruwa mai tarin yawa tare da dakile yawaitar ta'ammali da gishiri.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya 3.8m na iya fuskantar karancin abinci - Hukumomin Duniya sun yi gargadi

A cewar kungiyar lafiya ta duniya wato WHO (World Health Organisation), akwai kaso 11 cikin 100 na cutar koda a Najeriya da hakan yake nuna cewa akwai mutum daya cikin tara dake dauke da wannan cuta.

Bincike ya bayyana cewa, ciwon Koda yana barazana ga wadansu cututtukan da suka hadar da cutar hawan jini, ciwon sukari da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng