Hatsari ba sai a mota ba: Wata ma’akaciyar jirgin Emirate ta wuntsulo daga jirgin sama
Wata jami’ar walwalar Fasinjojin jirgin sama ta wuntsulo daga cikin jirgin sama wanda hakan yayi sanadiyyar samun munanan raunuka da suka jefa ta cikin halin rai fakwai mutu fakwai.
The Cables ta ruwaito wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Laraba 14 ga watan Maris, a filin sauka da tashin jirage na Entebbe dake kasar Uganda, daga jirgin da take aiki a ciki, EK 730.
KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta bankado wasu gwamnonin APC guda 8 dake yi ma Buhari ‘ingiza mai kan turuwa’
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jami’ar ta wuntsulo ne ta kofar gaggawa a lokacin jirgin ya sauke fasinja kenan, yana kokarin tashi ya wuce kasar Dibai, inda nan da nan aka garzaya da ita zuwa Asibiti.
Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da lamarin, inda guda yace an hangeta tana cacar baki da wasu daga cikin abokan aikinta a lokacin da suke shigewa cikin jirgin, “Gwiwowinta sun farfashe, haka zalika kofin gilashin da take rike da shi duk ya yayyanka mata jiki.” Inji shi.
Sai dai kaakakin hukumar kula da jiragen sama ta kasar Uganda, Vianney Luggya ta tabbatar da faruwar lamarin, amma fat ace za’a bincike musabbabin jin wuntsulowar jami’ar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng