Zazzaɓin Lassa ya hallakar da rayuka 3 a jihar Bauchi

Zazzaɓin Lassa ya hallakar da rayuka 3 a jihar Bauchi

A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamnatin jihar Buachi ta bayar da rahoton salwantar rayukan mutane uku, bayan da bincike ya tabbatar da mutane 25 masu dauke da cutar Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar.

Shugaban asibitocin duba gari na jihar, Alhaji Ibrahim Gamawa, shine ya bayar da wannan sanarwa a yayin bude taron fadakarwa tare da wayar da kawunan malaman asibiti a kan wannan cuta ta Lassa.

Zazzaɓin Lassa ya hallakar da rayuka 3 a jihar Bauchi
Zazzaɓin Lassa ya hallakar da rayuka 3 a jihar Bauchi

A cewar sa, jihar ta samu mutane 25 masu dauke da kwayoyin cutar tare da salwantar rayuka 3 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Maris.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Bikin cikar shekaru 81 na tsohon shugaba Obasanjo

Shugaban makiwatan lafiya na jihar ya bayar da jerin sunayen kananan hukumomin da annobar ta afkawa kamar haka; Alkaleri, Bauchi, Bogoro, Dass, Tafawa Balewa, Toro da kuma Warji.

Gamawa ya kuma fadakar da ma'aikatan na Lafiya akan wannan cuta da ka'idoji tunkarar ta kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin zagayowar ranar 'yancin kai na kasar Ghana tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel