Kiwon Lafiya: Amfanin Gishiri ga Lafiyar Dan Adam

Kiwon Lafiya: Amfanin Gishiri ga Lafiyar Dan Adam

Kamar yadda gama garin al'umma su ka san amfanin gishiri a matsayin mai kara dandado ga abincin mu na yau da gobe, ana kuma amfani da shi wajen bangaren kiwon lafiya sakamakon muhimman sunadari da sirrika da ya kunsa.

Masana kiwon lafiya su na la'akari da daidaiton dake tsakanin gishiri da kuma ruwa dake gudana a cikin jinin jikin dan Adam a matsayin inganci na lafiyarsa.

Gishiri
Gishiri

Gishiri wanda a kimiyance ake kiran sa da sunan Sodium Chloride, yana kunshe da sunadaran gina jiki tare da bayar da kariya ga lafiya da suka hadar da; Iodine, magnesium, potassium, calcium da kuma sodium.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta tanadi sabbin mahallai ga dakarun ta a jihar Neja

A sakamakon tabbarraki na wannan sunadarai, Legit.ng ta kawo hanyoyin inganta lafiya 7da gishiri ke taka rawar gani a jikin dan Adam kamar haka:

1. Inganta lafiyar zuciya.

2. Hana kamuwa da ciwon sukari wato Diabetes.

3. Taimako ga lafiyar masu juna biyu.

4. Hana kamuwa da cutar Cystic Fibrosis dake lahani ga hunhun kananan yara.

5. Tsarkake hakori da kwayoyin cututtuka na Bacteria.

6. Hana kumburi na tashoshin numfashi.

7. Warkar da radadi da bushewar makoshi.

Sai dai duk da wannan alfanu da gishiri ya kunsa, likitoci sun yi gargadi ketare adadin da ya kamata mutane su yi amfani da shi na gram 6 a kowace rana daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng