Gwamnatin jihar Kaduna ta kai ziyarar maraba ga Sarkin Zazzau bayan kwashe tsawon lokaci yana jinya a Ingila
- Sarkin Zazzun ya dawo Najeriya cikin koshin lafiya
- Sarkin Zazzau ya kwashe tsawon lokacin yana jinya a Ingila
A ranar Litinin 12 ga watan Maris ne dai mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya dawo daga kasar Ingila inda ya kwashe tsawon lokaci yana jinya,kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
A cikin satin data gabata ne dai gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya tabbatar da jinyar da Sarkin yake yi a kasar Ingila, inda ya bayyana cewa Sarki na gab da dawowa, sakamakon karin lafiya da yake samu.
KU KARANTA: Zaman lafiya: Wasu makiyaya sun mika ma Yansanda bindigunsu guda 30 a jihar Neja
A ranar Talata ne dai tawagar gwamnatin jihar Kaduna ta kai masa ziyarar maraba a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Barnabas Bala Bantex, inda suka bayyana godiyarsu ga Allah da ya dawo da Sarki lafiya cikin koshin lafiya.
A tare da mataimakin gwmanan jihar Kaduna Yusuf Barnbana Bala Bantex, akwai sakataren gwamnatin jihar Balarabe Abbas Lawal, kwamishinan kudi, Suleiman Kwari, Kwamishinan kananan hukumomi, Farfesa Kabir Mato da sauransu.
Daga karshe sun yi ma Sarki addu'ar Allah ya kara masa lafiya da tsawon kwana masu albarka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng