Kiwon Lafiya: Amfanin 'Kimchi' 8 ga lafiyar dan Adam
Shi dai Kimchi wani nau'in abinci ne da ya fi shahara a al'adar mutanen kasar Koriya, wanda ake hada shi ta hanyar turara ganyeyyaki irin su Kabeji tare da kayan hadi domin kari dandano da suka shafi gishiri, tafarnuwa, citta da sauransu.
Wannan nau'in hadadden abincin ya kunshi sunadarai masu tarin sirrika tare da taka rawar gani ga lafiyar masu ta'ammali da shi.
Sunadarai da Kimchi ya kunsa sun a hadar da; Fiber, Vitamin A, Vitamin B1, Vitamin B2, Vitamin C, Amino Acids, Iron, Calcium, Selenium da kuma Antioxidants irin su Flavonoids da sauransu.
KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta tanadi sabbin mahallai ga dakarun ta a jihar Neja
Legit.ng ta kawo muku jerin sirrika 10 da wannan abinci na Kimchi ya kunsa;
1. Narkar da daskararren mai a jikin mutum wato Cholesterol.
2. Rage nauyin jiki na dan Adam.
3. Inganta garkuwar jiki ga cututtuka.
4. Kariya ga cutar Daji wato Cancer.
5. Waraka ga ciwon sukari.
6. Kawar da gyambon ciki wato Gastric Ulcer.
7. Hana tsufa da wuri da taimakon sunadarin Vitamin C.
8. Waraka ga cutar nan ta fata mai sunan Dermatitis.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng