Ababen kiyayewa yayin amfani da Tafarnuwa wajen kiwatar lafiya
Da yawan mutane sukan ribaci alfanun dake kushe cikin tafarnuwa tun tala-tala wajen kiwatar lafiyar su. Akan yi amfani da ruwan tafarnuwa wajen kawar da cututtukan da suka shafi kirji inda take da matukar tasiri wajen kawar da cutar Kansa ta hunhu.
Binciken masana kiwon lafiya sun bayyana wasu sirrika da ya kamata a kiyaye wajen amfani da tafarnuwa domin cin ribar sunadaran kiyaye lafiya da ta kunsa. Akwai kura-kurai da dama da ya kamata a kiyaye yayin amfani da tafarnuwa.
Yana da kyau yin amfani da tafarnuwa a cikin girki wajen karin dandano da kamshi, sai dai kash dafa tafarnuwa ya kan rusa muhimmin sunadarin allicin da ta kunsa.
KARANTA KUMA: Rundunar Sojin kasa ta damke wasu makiyaya 3 a jihar Nasarawa
Sunadarin allicin shine tafarkin duk wani sirri da tafarnuwa ta kunsa, inda wasu kwararrun masana kiwon lafiya, David Winston da Merrily A. Kuhn suka tabbatar.
Masana kiwon lafiyar sun yi gargadin dafa tafarnuwa kafin amfani da ita, inda suka bayyana cewa hakan yana rusa duk wata rawa da sunadarin allicin yake takawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng