Labarin Sojojin Najeriya
A ‘yan kwanakin nan, ‘Yan ta’adda na kokarin karbe iko da wasu garuruwa. Yau aka ji ‘Yan Islamic State in West Africa Province sun tare motocin abinci a Borno.
Dakarun rundunar Operation hadin kai a cigaba da yaki da ta'addanci tare da hadin guiwar Operation Desert Sanity, sun halaka 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP.
Alkalin kotun laifuka na musamman, Justis Oluwatoyin Taiwo, ya yankewa Bolarinwa Abiodun, wani janar din soja na bogi hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.
An samu akasi, sojoji sun yi wa mutane ruwan bam-bamai a kauyen Katsina. Zuwa lokacin da muke tattara wannan labari, ba mu da adadin wadanda abin ya shafa.
Mu na da labari ‘Yan ta’addan da suka tare jirgin Abuja su na barazanar yanka wadanda suka dauke. Malam Tukur Mamu ya tabbatar da ingancin labarin da yake yawo.
A gaban idanun mutane ‘yan bindiga su ka kai hari ga tawagar shugaban Najeriya. Wani mutumi ya bada labarin yadda suka arce zuwa cikin daji domin su tsira.
Kwamandan Operation Hadin Kai da ke yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, Manjo Janar Christopher Musa, ya ce yan Boko Haram fiye da 60,000 ne suka mika wuya.
Dakarun Operation Safe Haven sun dakile yi nasarar dakile wani hari da yan bindiga suka kai garin Gajin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.
Rundunar sojojin sama tare da taimakon rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta kashe wasu mayakan ISWAP masu yawan gaske a karamar hukumar Marte da ke jihar Borno.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari