Wanda aka yi a idonsa, ya bada labarin yadda Miyagu suka aukawa Ayarin Shugaban kasa

Wanda aka yi a idonsa, ya bada labarin yadda Miyagu suka aukawa Ayarin Shugaban kasa

  • A gaban idanun mutane ne ‘yan bindiga su ka kai hari ga tawagar shugaba Muhammadu Buhari
  • A ranar Talata wadannan miyagu suka aukawa ‘yan tawagar shugaban Najeriya a garin Katsina
  • Wani mutumi ya bada labarin yadda suka arce zuwa cikin daji domin su tsira da rayuwarsu a jiyan

Katsina - Wani mazaunin garin Katsina wanda aka kai wa tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari hari a gabansa, ya bada labarin yadda ya sha da kyar.

Wannan Bawan Allah ya shaidawa Daily Trust cewa daji suka ruka ruga domin tsira da ransu.

A cewar wannan mutumi wanda abin ya kusa rutsawa da wasu, shi da wasu Bayin Allah sun boye ne a cikin jeji domin gudun ‘yan bindigan su auka masu.

Kamar yadda ya fadawa manema labarai a yamacin Talata, wannan mutum yake cewa su na kan hanyarsu ta dawowa Dutsinma daga Kankara ne abin ya faru.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Miyagun 'yan bindiga sun buɗe wa masu Jana'iza wuta a jihar Kaduna

'Yan bindiga a babura

Kwatsam sai ga ‘yan bindiga masu yawa su na tsallaka titi a kan babura, tuni su kuwa suka arce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin mutanen da suka hango miyagun sun tsere, sun shiga kauyen Turare, wasunsu kuma sun rabe a cikin daji, har sai da suka tabbata sun yi gaba.

Tawagar Shugaban kasa
Tawagar motocin shugaban Najeriya a Legas Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Daga cikin jejin ne wadanda suka samu wurin buyar suka hangi doguwar tawagar sojoji ta iso, wanda ta taimaka wajen buda masu hanya har zuwa Dutsinma.

Rahoton da jaridar ta fitar a daren Laraba, 5 ga watan Yuli 2022, ya nuna cewa daga cikin mutanen gari, babu wanda ‘yan bindigan suka harba ko suka hallaka.

An rasa babban Jami'i

A jiyan ne kuma aka tabbatar da cewa babban jami’in rundunar ‘yan sanda na shiyyar Dutsin ma, ACP Aminu Umar ya mutu a wani mugun harin ‘yan bindigan.

Kara karanta wannan

Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba

‘Yan ta’adda sun harbe Aminu Umar da wani yayin da suka yi wa 'yan sanda kwanton-bauna da suka je wani aiki a dajin Zakka da ke karamar hukumar Safana.

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa wannan yanki yana daga cikin mafi hatsari a Katsina. An saba jin an kashe Bayin Allah ko a sace su domin karbar kudi.

Abin bai yi muni ba

A jiya kun samu labari Malam Garba Shehu, ya ce tawagar da aka kai wa farmaki ta ƙunshi, hadimai, ma'aikata da yan jaridar gidan gwamnatin tarayya.

Mai girma Muhammadu Buhari bai cikin tawagar, amma an harbi wasu, yanzu haka wani na kwance a asibiti sakamakon harin da jami'an tsaro suka daƙile.

Asali: Legit.ng

Online view pixel