Da duminsa: Sojoji sun ragargaza kwamandojin Boko Haram, sun samo miyagun makamai

Da duminsa: Sojoji sun ragargaza kwamandojin Boko Haram, sun samo miyagun makamai

  • Zakakuran dakarun rundunar Operation Hadin Kai da Operation Desert Sanity, sun ragargaza manyan kwamandojin Boko Haram/ISWAP
  • Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Yulin 2022 a kan babbar hanyar Dikwa zuwa Gamboru dake jihar Borno
  • Kamar yadda shafin rundunar sojin kasa ya bayyana a Twitter, sun yi nasarar kwace miyagun makamai daga mayakan ta'addancin

Borno - Dakarun rundunar Operation hadin kai a cigaba da yaki da ta'addancin da suke yi tare da hadin guiwar Operation Desert Sanity, sun halaka manyan 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP da suka hada da manyan kwamandojinsu a jihar Borno.

A shafin rundunar sojin kasan na Twitter, sun sanar da wannan cigaban da aka samu a ranar Alhamis, 7 ga watan Yulin 2022 a kan babbar hanyar Dikwa zuwa Gamboru a jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, ya dira gidan yarin Kuje

Sojojin Najeriya
Da duminsa: Sojoji sun ragargaza kwamandojin Boko Haram, sun samo miyagun makamai. Hoto daga @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Dakarun sun sanar da cewa, sun kwace makamai masu tarin yawa na 'yan ta'addan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asali: Legit.ng

Online view pixel