Yankin arewa: Dakarun soji sun kashe kasurguman masu garkuwa da mutane biyu, sun ceto matafiya 9

Yankin arewa: Dakarun soji sun kashe kasurguman masu garkuwa da mutane biyu, sun ceto matafiya 9

  • Dakarun sojojin Operation Safe Haven sun halaka wasu kasurguman masu garkuwa da mutane, Abdulrazaq Umar da Idris Abdullahi
  • Umar da Abdullahi na cikin masu garkuwa da mutanen da suka addabi al'ummar jihohin Bauchi da Plateau
  • Sojojin da taimakon jami'an yan sandan jihar Plateau sun kuma yi nasarar ceto matafiya tara da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

Dakarun Operation Safe Haven sun kashe wasu kasurguman masu garkuwa da mutane biyu sannan sun kama masu fashi da makami biyu tare da ceto matafiya tara a yankin arewacin kasar.

Daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Bayan kwanaki 103, an fito da wasu fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja

Dakarun sojoji
Yankin arewa: Dakarun soji sun kashe kasurguman masu garkuwa da mutane biyu, sun ceto matafiya 9 Hoto: aceworldpub.com.ng
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa sun samu nasara a ayyukan da suka gudanar tare da jami’an yan sanda a tsakanin Alhamis da Asabar na makon da ya gabata a kokarinsu na ganin an yi bikin sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Musamman a ranakun 7 da 8 ga watan Yulin 2022, dakarun Operation Safe Haven, tare da hadin gwiwar yan sandan jihar Plateau, sun kama wasu kasurguman masu garkuwa da mutane, Abdulrazaq Umar da Idris Abdullahi, a yankin Beco Junction Heipang, karamar hukumar Barkin Ladi, jihar Plateau.
“Wadanda ake zargin sun aiwatar da ayyukan garkuwa da mutane da dama a tsakanin jihohin Plateau da Bauchi, ciki harda kisan Alhaji Saleh Abdulhamid (Shaba) a kauyen Ex-land a ranar 22 ga watan Yuni.”

A cewar kakakin rundunar sojin, wadanda ake zargin sun kuma bayyana wani Mallam Buhari Umar a matsayin shugaban kungiyarsu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

“Sai dai kuma a yayin zuwa mafakar miyagun, wadanda ake zargin sun yi yunkurin tserewa inda aka kashe su,” In ji shi.

Onyeuko ya bayyana cewa dakarun sun guma kai mamaya a Mailafia, Nisama, Dogon Filli da Gidan Waya duk a karamar hukumar Jema’a da ke jihar Kaduna.

A yayin aikin, ya bayyana cewa dakarun sun kama wasu yan fashi da makami biyu masu suna George Yakubu da George Joseph.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda uku, wuka, da sauransu, rahoton The Sun.

Kakakin sojin ya kuma ce:

“Haka zalika, a wannan rana, sojoji sun amsa kira cewa yan bindiga sun farmaki wata motar bas Toyota Hummer mai lamba ‘LFA 322 YR Nasarawa’ a kauyen Dogon Filli da ke karamar hukumar Jema’a.
“An tura sojoji wajen sannan suka ceto fasinjoji tara wadanda aka yi garkuwa da su. Rundunar sojin ta yabama dakarun Operation Safe Haven kan kokarinsu sannan ta bukaci jama’a da su taimakawa dakarun da bayanai abun dogaro a kan lokaci kan ayyukan yan ta’adda.”

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

'Yan fashi: Matawalle ya bukaci da a tsawaita shekarun ritaya na jami'an tsaro zuwa 70

A wani labari na daban, gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin ritayar jami’an tsaro a Najeriya zuwa shekaru 70, inda ya kara da cewa ya kamata a tsawaita shekarun shiga aikin Short Service daga shekaru 30 zuwa 32 domin samun karin ma’aikata.

Rahoton jaridar PUNCH Sai kuma a ba wa maza da mata masu karfi jiki dake son shiga aikin jami’an tsaro damar yi wa kasar su hidima don tabbatar da tsaro a Najeriya.

Gwamna Matawalle wanda ya yi jawabi a gidan sa da ke Maradun, ya ce hakan zai sa wadanda ba su gajiyawa su ci gaba da yi wa kasa hidima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel