Labarin Sojojin Najeriya
Rahotanni daga jihar Sakkwato sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi kwantan bauna, inda suka yi nasarar hallaka gwarazan jami'ai sun kai guda shida.
Jami'an tsaro sun kama Hamza Suruddubu, babban mai safarar makamai ga 'yan bindiga a Sokoto, wanda ake zargi da samar wa Bello Turji da abokan aikinsa makamai.
Shugaban sojojin Najeriya, Oluyede ya kai ziyara a Zamfara don duba matsalar tsaro, karɓar bayanai daga kwamandoji, da karfafa gwiwar dakarun fagen fama.
Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ce suna bin Bello Turji sau da kafa domin kawar da shi. Ana bin diddin dan ta'addar a Zamfara.
Gwamnatin jihar Katsina ta yabi sojoji kan nasarar kashe 'yan bindiga 53 da aka kai farmaki maboyar dan bindiga Buzuru da ya shahara da kai hare hare a jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan wasu 'yan bindiga da suka shahara da kai hare hare a Sabon Birni. Wani da aka ceto ya bayyana yadda maboyar ta ke.
Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan zaegin cewa jirgin yaƙinta ya hallaka fararen hula a wani hari da ya kai a jihar Katsina.
Dakarun rundunar sojojin sama na Najeriya sun jefa bam kan bayin Allah bisa kuskure a jihar Katsina. Mutane sun rasa rayukansu sakamakon jefa bam din.
Sojojin OPSH sun kashe masu garkuwa da mutane biyu, sun ceto mutum hudu a Jema’a, Kaduna, tare da kwato bindiga, harsasai, wayoyi da kudi har N1m.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari