Labari mai zafi: Bayan kwanaki 103, an fito da wasu fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja

Labari mai zafi: Bayan kwanaki 103, an fito da wasu fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja

  • ‘Yan ta’addan da suka tare jirgin kasan Abuja-Kaduna, sun saki wasu cikin wadanda suka dauke
  • A yau aka samu labari an sake ceto mutane bakwai, daga cikinsu akwai Sadiq Ango Abdullahi
  • Ubangiji ya yi wa Muhammad Paki, Bosede Rotimi, Abubakar Zubairu, da Hassan Sule gyadar doguwa

Kaduna - Bayan an dade ana tattaunawa, an yi nasarar ceto wasu daga cikin fasinjojin da aka dauke a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna tun watan Maris.

Leadership ta fitar da rahoto cewa Malam Tukur Mamu (Dan-Iyan Fika) shi ne ya taka rawar gani wajen ganin ‘yan ta’adda sun fito da wadannan mutane.

Malam Mamu wanda ya nemi ya hakura da maganar sulhu da ‘yan bindigan, shi ne dai ya yi sanadiyyar da mutum bakwai suka kubuta a karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

Sadiq Ango Abdullahi yana cikin wadanda suka shaki iskar ‘yanci yayin da ake murnar bikin sallah a Najeriya. Mahaifinsa shi ne Farfesa Ango Abullahi.

Sadiq Ango da mutum 6 sun sha

Baya ga ‘dan siyasar, rahoton da aka fitar a ranar Asabar, ya tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun fito da Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran fasinjojin da za su kwana a gida yau sun hada da; Muhammad Daiyabu Paki, Aliyu Usman da wani ‘dan kasar Fakistan, Dr. Muhammad Abuzar Afzal.

Jirgin-kasan-abuja-kaduna
Jirgin Kaduna-Abuja
Asali: UGC

Da yake magana, Mamu ya ce nasarar da aka samu wajen ceto mutanen nan ya kara nuna abin da Sheikh Ahmad Gumi yake fada a game da karfin yin sulhu.

“Ina so in tabbatarwa kasar nan an samu nasarar da aka samu a yau ne saboda kokarin da na fara, tare da goyon bayan mai gidana, Sheikh Ahmad Gumi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

Amfanin sulhu da miyagu

Shi ya sa na rika jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta na da ikon da za ta iya kawo karshen zulumin da wadannan mutane suke ciki a cikin a rana daya.
Wannan kokarin mutum daya kenan da ya saida rayuwarsa da ma darajarsa. Karfin soja kadai ba zai ia shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya."

- Malam Tukur Mamu

Daily Trust ta rahoto Mamu yana cewa idan aka zauna da ‘yan ta’addan, za su saurari mutane.

Da yake jawabi dazu, an rahoto Dan Iyan na Fika ya ce wadanda aka saki su na hannun jami’an sojoji, kuma su na kan hanyarsu na zuwa Kaduna a yanzu.

Za a yanka wadanda aka kama

Ku na da labari cewa an faifai yana yawo da aka ji wani fasinjan jirgin kasan Kaduna-Abuja yana kukan cewa ana barazanar za ayi masu yankon raho.

Wannan mutumi da ke tsare a hannun miyagun ‘yan ta’adda, ya ce an fara maganar za a yanka su, muddin ba a biyawa 'yan ta'addan bukatar da suke nema ba.

Kara karanta wannan

Mai dakina ta na ajiye Bible dinta a gefen Qur’ani na, kuma a kwana lafiya inji Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel