Jirgin Sojoji ya samu akasi, an yi wa Bayin Allah wuta ana zaune kalau a Katsina

Jirgin Sojoji ya samu akasi, an yi wa Bayin Allah wuta ana zaune kalau a Katsina

  • An samu tangarda a Katsina inda wani jirgin yakin ya aukawa wadanda ba su san hawa da sauka ba
  • Jirgin sojojin sama ya yi barin wuta a wani kauye da ke Safana a kokarin hallaka ‘yan ta’adda
  • Tun da abin ya faru a ranar Talata, har yanzu Jami’an tsaro ba su fito sun iya yin wani jawabi ba

Katsina - Rahotanni na nuna cewa an rasa rayuka baya ga rauni da wasu suka samu a sakamakon akasin da aka samu daga wani jirgi na sojojin sama.

The Guardian ta ce wani jirgin saman rundunar sojojin Najeriya ya yi kuskuren dasa bam a wai kauye da ake kira Kunkuna a garin Safana, jihar Katsina.

A ranar Talata, 5 ga watan Yuli 2022, da kimanin karfe 11:00 na safe, ake tunanin jirgin sojojin ya aukawa mutane da tunanin cewa ‘yan ta’adda ne.

Kara karanta wannan

Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama

Abin ya faru ne jim kadan bayan an kai wa ayarin motocin shugaban kasa hari a hanyar Dutsinma.

An kai wa ayari hari

Tsakanin kauyen Yantumaki da garin Dutsinma ne ‘yan ta’adda suka rutsa tawagar shugaban kasa. Wannan ya sa sojoji suka budawa ‘yan bindigan wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Garin Safana yana kan iyaka ne da Dutsinma, kuma ‘yan bindigan da suke ta’adi a yankin, sun saba samun mafaka a dajin nan na Zakka a cikin Safana.

Jirgin Sojoji
Wani Jirgin sojojin saman JF-17 Hoto: nationalinterest.org
Asali: UGC

Rahoton ya ce jirgin sojojin yana kokarin buda wuta ga wadanda suka kai wa ayarin Mai girma shugaban kasa hari ne aka samu tuntube, aka aukawa jama’a.

An samu rashi sosai

Ana zargin cewa bama-baman da aka saki sun tashi, sun kuma kashe wasu da-dama a kauyen. Haka zalika wasu sun jikatta a sakamakon ruguza gidajensu.

Kara karanta wannan

Ana tsoron ‘Yan bindiga sun aukawa gidan yarin Kuje, inda DCP Abba Kyari su ke daure

Ko da har yanzu jami’an tsaro ba su ce uffan ba, Sahara Reporters ta tabbatar da wannan labarin.

‘Yan jaridar sun nemi jin ta bakin Mai magana da yawun bakin sojojin sama na kasa, Edward Gabkwet, amma bai amsa kiran da aka yi masa a waya ba.

Ko da muke tattara rahoto, ba mu da adadin wadanda abin ya shafa. Wata majiya ta ce mana an kai wadanda suka samu rauni zuwa asibitin garin Katsina.

Matsala ko ta ina

A makon nan ne aka ji labari cewa wani faifai yana yawo da aka ji fasinjan jirgin kasan Kaduna-Abuja da aka dauke su yana kukan ana barazanar kashe su.

Ana haka kuma sai ga rahoto ‘yan ta’addan Boko Haram sun aukawa gidan yarin Kuje, inda wasu abokan aikinsu suke daure, a karshe dai dukkansu sun tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel