Labaran Duniya
Wasu ‘yan dabar Hindutva sun hari limamin wani masallaci ta hanyar watsa mishi asid. Kamar dai yadda aka sani, akwai wata zanga-zanga da Musulman kasar India ke yi sakamakon banbancin da ake nuna musu tun a watan Disamba na 2019..
Wani tsohon dan asalin kasar Japan mai suna Chitetsu Watanabe wanda aka bayyana shi a matsayin mutumin da ya fi kowa yawan shekaru a duniya ya mutu yana dan shekara 112.
An samu barkewar cutar coronavirus karo na farko a nahiyar Afirka. Ministan kiwon lafiya na kasar Algeria din ne ya sanar da cewa an samu mutum na farko mai dauke da mummunar cutar a kasar...
Hukumomin wasanni na kasar Saudiyya sun fitar da kungiyar kwallon kafa ta mata. Duka dai wannan na zuwa ne a kokarin da Yariman kasar mai jiran gado, Mohammed bin Salman yake yi na ganin ya zamanantar da kasar a idon duniya...
Wani likita a kasar Tanzaniya mai suna Jj Mwaka ya bayar da labarin yadda aka yi ya kare da auran mata uku. Mutumin na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin matansa uku.
Wani mutumin kasar Japan da aka ambata a matsayin namijin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekara 112, wata hukumar kasar ta bayyana a ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu.
Gwamnatin kasar China a ranar Litinin ta haramta ci ko kasuwancin naman dabbobin daji a matsayin hanyar kare kiwon lafiyar jama'a. Hakan ya biyo bayan danganta cutar Covid-19 da aka yi da cin naman dabbobin daji...
Caro Nduti mazauniya Nairobi ce mai shekaru 38 a duniya. Ta ce babu abinda ba ta gani ba fannin aure. Ta ga soyayya, yaudara, cin amana da kuma cin zarafi. Amma babban laifinta shine yadda ta so shi da yawa...
Jami'ai daga kasar Saudi sun bukaci kama wata mawakiyar gambara a kan wata bidiyon waka da ta saki cikin kwanakin nan. A bidiyon wakar mai suna 'Yan matan Makka', mawakiyar mai suna Ayasel Slay a kasar Saudi din ta saka riga...
Labaran Duniya
Samu kari