Lamari ya kai intaha: Dogarai sun yiwa Dan sanda dan karen duka saboda yaki bin dokar Sarauniya

Lamari ya kai intaha: Dogarai sun yiwa Dan sanda dan karen duka saboda yaki bin dokar Sarauniya

- Wani bidiyo da ya fada yanar gizo ya ba mutane masu tarin yawa mamaki

- A bidiyon an ga masu tsaron fada na hantarar wani dan sandar kasar Ghana sakamakon karya doka da yayi

- Dan sandan ya karya dokar da aka gindaya ne yayin birne babbar sarauniyar masarautar Sunyani da ke Ghana

Wasu masu tsaron fada sun ci zarafin wani dan sanda sakamakon take dokar da aka gindaya da yayi yayin bikin birne sarauniyar Sunyani, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Wani dan sandan kasar Ghana ya samu cin zarafi mai yawa daga masu tsaron fadar masarautar Sunyani. Sun zargesa ne da karantsaye ga dokar da aka gindaya a yayin birne babbar sarauniyar masarautar.

An gano cewa tuni aka ja kunnen jama’a a kan tafiya ta wani waje tare da saka wasu irin kaya duk a cikin shirye-shiryen bikin.

A wani bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an ga masu tsaron fadar na tsangwamar dan sandan sakamakon take dokar da yayi.

KU KARANTA: Ba wani kokari da gwamnatin Najeriya take yi wajen kawo karshen Boko Haram - Kasar Faransa

Amma kuma mutane da yawa sun yi mamakin yadda jami’an tsaron kasar Ghana din suka zuba ido yayin da masu tsaron fada ke tsangwama, hantara da cin zarafin abokin aikinsu.

A wani labara na daban, an ji yadda wani barawo ya more gumin wasu ‘yan sanda. ‘Yan sandan na tsaye ne a titi inda suke amsar na shan ruwa daga masu ababen hawa, yayin da shi kuwa barawon ya fito daga wani daji da ke gefensu tare da wabce ledar kudin da suka tara.

Kamar yadda jaridat Pulse.ng ta bayyana, ‘yan sandan sun bi barawon da zagi tare da Alllah ya isa bayan da suka gane ba zasu iya kama shi ba. Hakazalika, suna dauke ne da kulki a maimakon bindigogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel