Matashi ya kashe kanshi bayan tsangwamar da mutane ke yi masa, saboda ya zama dan luwadi

Matashi ya kashe kanshi bayan tsangwamar da mutane ke yi masa, saboda ya zama dan luwadi

- Wani yaro mai shekaru 16 ya kashe kan shi ta hanyar rataya sakamakon tsangwamar da yake fuskanta daga wajen dalibai ‘yan uwan shi

- Tun yana da shekaru 12 a duniya, Cameron Warwick ya bayyana cewa namiji ke ba shi sha’awa don haka dan luwadi ne shi

- A ranar 5 ga watan Satumba ne aka duba Warwick ba a gan shi a makaranta ba sai aka tsinci gawar shi a daji inda ya sagale kan shi

Wani yaro mai shekaru 16 ya kashe kan shi sakamakon tsana da hantarar da yake samu don yana luwadi.

Yaron mai karancin shekaru ya fito ya bayyana halin da yake ciki ne a lokacin da ya cika shekaru 12 a duniya. Hakan kuwa ya ja mishi tsana daga abokan karatun shi. Cameron Warwick na fama da wani hali na rashin iya shiga mutane. Hakan ya kara taka rawar gani wajen sa mishi kunci.

Matashi ya kashe kanshi bayan tsangwamar da mutane ke yi masa, saboda ya zama dan luwadi
Matashi ya kashe kanshi bayan tsangwamar da mutane ke yi masa, saboda ya zama dan luwadi
Asali: Facebook

An gano cewa wani yaro mai shekaru 16 ya kashe kan shi ne bayan tsangwamnar da yake fuskanta a makaranta saboda dan luwadi ne, kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

Cameron Warwick dan asalin Fareham ne a Hamspshire kuma an samu gawar shi ne a Fort Fareham Woods a ranar 5 ga watan Satumba. Yaron ya fito a matsayin da luwadi tun yana da shekaru 12 kuma hakan yasa ‘yan makarantarsu suka dinga tsangwamar shi, in ji mahaifiyar shi.

KU KARANTA: Kwamacala: Mijina mai kanjamau ya auri 'ya ta, sun kuma hada baki sun kore ni daga gidan - Mata ta koka

Warwick bai cika son shiga mutane ba wanda hakan yasa yake fama da kunci. Mahaifiyar shi Kerry Warwick mai shekaru 38, ta ce hakan ya kai ga har dalibai na watsa mishi abinci. Hakan yasa ya kasa jure wannan tsangwamar.

Daliban kan tsare shi a kan hanya don zagin shi. Rashin sabawa da mutane na daga cikin abinda ya kara mishi kunci wanda hakan yasa ya dauki rayuwarshi.

“Wani yaro ya taba ce mishi ba shi da kyau saboda bai boye halin da yake ciki ba. Cameron ya fadi jarabawar GCSE don shiga karatun wasanni na makaranta saboda halin da yake ciki,” in ji wani abokin shi mai suna Kerry.

A ranar 5 ga watan Satumba ne ba a ga Cameron a makaranta ba. Daga baya sai aka tsinci gawar shi a sagale ya rataye kan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng