Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya mutu yana da shekara 112

Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya mutu yana da shekara 112

Wani mutumin kasar Japan da aka ambata a matsayin namijin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekara 112, wata hukumar kasar ta bayyana a ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu.

Chitetsu Watanabe, wanda aka Haifa a ranar 5 ga watan Maris, 1907 a Niigata, arewacin Tokyo ya mutu a ranar Asabar, a gidan rainonsa da ke yankin, in ji hukumar.

Labarin na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan kundin tarihi na duniya ta Guinness World Records ta karrama shi.

Watanabe, wanda ke da yara biyar, ya ce sirrin tsawon rai ya kasance “rashin fushi da yawan sanya murmushi a fuskar mutum.”

Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya mutu yana da shekara 112
Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya mutu yana da shekara 112
Asali: UGC

A yanzu mutum mafi tsufa a Japan ya kasance Issaku Tomoe, wanda ke da shekara 110, a bisa ga rahoton Jiji Press, koda dai babu tabbacin ko Tomoe ne ke rike da wannan matsayi na duk duniya

Mutum mafi tsufa ma yar Japanese ce, Kane Tanaka, wacce ked a shekara 117.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kashe yan fashi 5 a musayar wuta da suka yi a Katsina

Japan ta kasance daya daga cikin wurare da aka fi samun masu tsawon rai a duniya kuma ta kasance kasar mutane da dama da aka bayyana cikin mutane mafi tsufa da aka taba samu a duniya.

Sun hada da Jiroemon Kimura, wanda ya rikin kanbun mutum mafi tsufa, wanda ya rasu bayan ya yi shekara 116 a watan Yuni 2013.

A wani labari na daban, mun ji cewa an kama wani mutum mai shekara 42, Emmanuel Osiben kan zargin soke abokinsa mai shekara 38, Femi har lahira yayinda ya ke kokarin karban bashin naira 1,200 da ya ke binsa.

Sai dai Osiben wanda ya mallaki wani cibiyar kallo a yankin Ijora-Badia da ke Lagas, ya yi zargin cewa marigayin ne ya fara kai masa hari da kwalba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yanzu haka ana nan a tsare mai laifin a sashin binciken masu laifi, da ke Panti, Yaba kan aikata kisan kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng