Wata sabuwa: Mabiya addinin Hindu sun watsawa wani Limamin Masallaci guba a fuska

Wata sabuwa: Mabiya addinin Hindu sun watsawa wani Limamin Masallaci guba a fuska

- Wasu bata-gari ko kuma ‘yan daba mabiya addinin Hindutva sun hari limamin wani Masallaci a kasar India

- Bata-garin sun yi wa limamin masallacin mai shekaru 54 mugun duka ne tare da watsa mishi gubar asid a fuska

- Ba tun yau ba dai aka fara dauki ba dadi tsakanin Musulman kasar Iindia da mabiya sauran addinai a kasar

Wasu ‘yan dabar Hindutva sun hari limamin wani masallaci ta hanyar watsa mishi asid.

Kamar dai yadda aka sani, akwai wata zanga-zanga da Musulman kasar India ke yi sakamakon banbancin da ake nuna musu tun a watan Disamba na 2019.

A jiya ne kuma jaridar Loveforislamic ta walllafa , inda aka tattauna a kan hargitsi da ke aukuwa tsakanin Musulman kasar India da kuma bata-gari.

Wata sabuwa: Mabiya addinin Hindu sun watsawa wani Limamin Masallaci guba a fuska
Wata sabuwa: Mabiya addinin Hindu sun watsawa wani Limamin Masallaci guba a fuska
Asali: Facebook

Wani abu mai tarin ban mamaki ya faru a babban birnin New Delhi a ranar 27 ga watan Fabrairu na 2020. Wani limami ne mai shekaru 54 ne ya sha mugun duka a masallacin Shiv Vihar kafin daga bisani a yayyaga kayan shi tare da watsa mishi asid a fuska.

KU KARANTA: Binciken masana: Nan da shekarar 2050 yawan 'yan Najeriya zai kai miliyan 401

Akwai bukatar duk musulman duniya su taya musulman kasar Indai addu’a a masallatai, salloli da kuma sallolin dare. A kara da neman musu yafiyar Ubangiji a kan zunubbansu.

Babu cikakken bayani game da mutuwar mutane 30 da aka samu a birnin New Delhi din.Da yawa dai an ce wadanda suka rasa rayukan nasu mata ne da kananan yara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel