Ba wani kokari da gwamnatin Najeriya take yi wajen kawo karshen Boko Haram - Kasar Faransa

Ba wani kokari da gwamnatin Najeriya take yi wajen kawo karshen Boko Haram - Kasar Faransa

- Jakadan kasar faransa a Najeriya, Jerome Pasquier ya ce gwamnatin Najerriya ba ta yin abinda ya dace don kawo karshen rashin tsaro

- Pasquier ya ce akwai abubuwa masu yawa da ke damun yankin Arewa maso gabas din kasar nan a shekaru da yawa

- Ya ce shawo kan matsalar na bukatar samu isasshen bayani, tuntubar kwararru da kuma sauya salon yaki tunda tsohon salon ya ki kawo sakamako

Jakadan kasar Faransa a Najeriya, Jerome Pasquier ya ce gwamnatin Najeriya ba ta yin abinda ya dace don kawo karshen kalubalen tsaro a fadin kasar nan.

Pasquier ya sanar da hakan ne a ranar 26 ga watan Fabrairu yayin da yake jawabi a wani taron horarwa mai taken “Shawo kan matsalar tsaro a karkara da tashin hankali a yankin Arewa maso gabas na Najeriya”, wanda aka hada tare da hadin guiwar ofishin jakadancin kasar Faransa.

Ba wani kokari da gwamnatin Najeriya take yi wajen kawo karshen Boko Haram - Kasar Faransa
Ba wani kokari da gwamnatin Najeriya take yi wajen kawo karshen Boko Haram - Kasar Faransa
Asali: Facebook

Jakadan kasar Faransan, wanda ya samu wakilcin Ellien helios a taron, yayi kira ga hukumomin kasar nan tare da masu ruwa da tsaki a kan su kawo sabbin hanyoyin shawo kan rashin tsaron da ya addabi kasar nan.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kama ta saka saurayinta a cikin jaka ta datse da mukulli har sai da ya mutu

Ya ce; “Akwai abubuwa masu yawa da ke damun yankin Arewa maso gabaa din kasar nan a shekaru da yawa. Akwai kuma masu assasa lamarin, amma bana tunanin akwai abinda ake yi kan masu assasawa. An kasa samo dabarun shawo kan matsalar da halin da mutanen yankin ke ciki.

“Muna da wata damar aiki da sauraron mutane da suka hada dabaru kuma kwararru a kan harkar tsaro. Toh kamata yayi mu yi amfani da damar da muke da ita tare da samun isasshen ilimin matsalar, tsarin da zamu yi amfani da shi, habaka hanyar shawo matsalar da kuma kara kaimi.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel