Tashin hankali: A karon farko an samu mai cutar Coronavirus a nahiyar Afrika

Tashin hankali: A karon farko an samu mai cutar Coronavirus a nahiyar Afrika

- Kasar Algeria ta sanar da barkewar cutar Coronavirus karo na farko a nahiyar Afirka

- Ministan lafiyar kasar, Shamsuddin Shito ya sanar da cewa an samu mutum daya a kasar da cutar

- Sanannen abu ne dai cewa cutar ta barke a kasar Itali ta Arewa wacce ke dauke da ‘yan Algeria masu tarin yawa

An samu barkewar cutar coronavirus karo na farko a nahiyar Afirka. Ministan kiwon lafiya na kasar Algeria din ne ya sanar da cewa an samu mutum na farko mai dauke da mummunar cutar a kasar.

Shamsuddin Shito, ministan lafiyan kasar Algeria ya sanar da cewa an samu mai cutar sakamakon tsananin binciken da aka saka a kan tudu da ruwa da kuma duk wata hanyar shiga kasa.

Tashin hankali: A karon farko an samu mai cutar Coronavirus a nahiyar Afrika
Tashin hankali: A karon farko an samu mai cutar Coronavirus a nahiyar Afrika
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa wani dan asalin kasar Itali ne wanda ya isa kasar a ranar 17 ga watan Fabrairu ke dauke da cutar. An kuma ware mutumin don bashi magani da kulawar da ta dace.

Ya yi kira ga ‘yan kasar Algeria da su kiyaye duk wani bayani da zasu yada a yanar gizo a kan cutar.

KU KARANTA: Maza masu mace daya suna rayuwa rabi da rabi ne - Cewar tsohon dan takarar shugaban kasa

Shitor ya ce; “An samu mutum daya da aka tabbatar yana dauke da kwayar mummunar cutar ta coronavirus daga cikin mutane biyun da aka zargi suna dauke da ita. Dukkansu kuwa ‘yan asalin kasar Itali ne.

“Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da aka tabbatar da dan asalin kasar Masar din da aka kebance ya bayyana baya dauke da cutar.”

Arewacin Itali dai kasa ce ta ke dauke da ‘yan kasar Algeria masu tarin yawa kuma suna fuskantar barkewar muguwar cutar har da rasa rayuka 11.

Cutar dai ta fara barkewa ne a birnin Wuhan da ke kasar China inda a halin yanzu ta shafi mutane 80,000 a duniya tare da kashe 2,700.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel