Babbar magana: Yadda na dinga sanya kanwata tana kwanciya da mijina - Matar aure

Babbar magana: Yadda na dinga sanya kanwata tana kwanciya da mijina - Matar aure

- Caro Nduti mace ce mai shekaru 38 kuma mahaifiyar yara maza biyu

- Caro ta bayyana rayuwar soyayya, yaudara, cin amana da cin zarafi data fuskanta sakamakon soyayyar da ta nuna wa mijinta

- Neman matan mijinta yayi yawan da har 'yar uwarta yake nema kuma suka haifa yara biyu da ita

Caro Nduti mazauniya Nairobi ce mai shekaru 38 a duniya. Ta ce babu abinda ba ta gani ba fannin aure. Ta ga soyayya, yaudara, cin amana da kuma cin zarafi. Amma babban laifinta shine yadda ta so shi da yawa.

Nduti ta fara bada labari ne tun lokacin da take kwaleji a Nairobi da ta fara soyayya da abokinta. A 2002 ne suka fara makarantu mabanbanta amma hakan bai raba soyayyarsu ba. Daga baya kuwa sai suka koma zama tare.

"Saurayina ya bukaci mu haihu kafin mu kammala karatu saboda yana tsoron zan bar shi idan na kammala karatuna," Nduti ta sanar da BBC.

"Ina son shi sosai shiyasa na amince da wannan hukunci kuma na samu ciki," Nduti ta ce.

Ta haifa yaro namiji bayan watanni da kammala karatunta. Soyayyarsu kuwa tayi karfi don har ya kaita dangin shi a matsayin wacce zai aura.

"A lokacin, saurayina na matukar sona da kaunata," Nduti ta ce.

A 2006 kuwa ta kara haihuwar da namiji amma sai ta gano mijinta ya canza. Ta gano cewa yana neman mata. Saboda yarinta a lokacin, ta kasa yi mishi maganar.

"Duk da neman matan shi, yana bani duk abinda nake bukata. A ganina toh me zai sa in yi korafi? A tunanina dole ne in jure," ta ce.

"Wasu daga cikin matan da yake lalata dasu duk na san su. Daga baya sai ya fara neman wata 'yar uwata wacce muka tashi tare. Mahaifiyata ce ta rike ta bayan mutuwar mahaifiyarta lokacin tana da shekaru 7," ta ce.

"Wulakancin mijina har ya kai ga yana kirana a kan ba zai dawo gida ba don zai kwana a wajen 'yar uwata," Nduti ta ce.

Daga nan kuwa 'yar uwarta ta fara gadara tare da zaginta a gabanta. Shi kuwa mijinta ya kasa daukar mataki a kan hakan. Akwai lokacin da ya sanar da ita cewa bai ga dalilin da yasa 'yar uwarta ba za ta dinga zaginta ba.

A 2008, Nduti ta bar gidan mijinta amma ya dawo ya lallabata ta kuma koma. "Mun koma rayuwa tare da 'yar uwar tawa kuma ina zama ne saboda 'ya'yana. 'Yar uwata ta haihu har sau biyu, kuma duk na mijina ne." Ta ce.

A yayin da take kokarin raba 'yar uwarta da mijinta, yana can yana bibiyar duk wata 'yar aiki da ta kawo gidan. Bayan komai ya isheta ne ta bar auren inda suka rabu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel