Magidanci ya bayyana dalilin da yasa yake kwana da matansa 2 cikin 3 a gado daya

Magidanci ya bayyana dalilin da yasa yake kwana da matansa 2 cikin 3 a gado daya

Wani likita a kasar Tanzaniya mai suna Jj Mwaka ya bayar da labarin yadda aka yi ya kare da auran mata uku.

Mutumin na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin matansa uku sannan cewa bai taba samun farin ciki irin na yanzu ba.

Da yake magana a wata hira da Clouds Media tare da rakiyan matansa na biyu da uku, likitan ya ce hadama ne ya kai shi auren mata fiye da guda daya, wanda ya zama halin maza.

A cewarsa, ya auri matarsa ta biyu ba tare da sanin uwargidarsa ba amma daga bisani sai ya gaji da boye matar tasa ta biyu inda ya yanke shawarar sanar da uwargidar tasa.

Matar tasa ta biyu ta ce ta san da batun matarsa ta farko sannan cikin lumana ta sanar mata da ko ita wacece inda suka saba da junansu.

Matar ta biyu ta kuma bayyana yadda suka gano batun mata ta ukun. Ta ce da farko ita da matar ta farko sun zata na dan lokaci ne zai wuce.

Bayan dan wani lokaci, sai matar ta farko ta bayyana wa mata ta biyun cewa da gaske ne abun.

“A lokacin hutunmu inda muke haduwa a matsayin iyali sai kishiyata ta sanar dani cewa alaka ce mai karfin gaske sai muka yanke shawarar gano inda take,” in ji matar ta biyu.

“Mun je gidanta amma sai bamu same ta ba. Don haka sai muka yi hotuna da yaranta Sannan muka daura a shafukanmu na zumunta don nusar da mijinmu cewa mun gano sirrinsa.”

Mijin kasancewarsa wayayyen mutum sai ya yi gaggawan wallafa hotunan matan nasa a shafin Instagram don sammatan matansa biyu wanda hakan ya kara kawo rikici.

Matar ta biyu ta ce sun yi hannun riga na tsawon wani lokaci amma daga bisani ta yanke shawarar haduwa da matar ya uku domin amsarta kamar yadda ta farkon ta amshe ta hannu bibbiyu.

Sai suka zamo aminan juna sannan tun daga lokacin suke cikin farin ciki.

Likitan ya kuma bayyana cewa gidajensu daban daban amma su kan kwana tare a gado daya da matarsa ta biyu da ta uku idan suna tare.

KU KARANTA KUMA: Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya mutu yana da shekara 112

Ya ce hakan ba zai faru ba da matarsa ta biyu saboda yawan shekaru da tarin kimarta da suke gani don ta girme masu.

“Muna kwana tare da matana na baya-baya amma ba da na farkon ba saboda banbancin shekarunsu da tazara sosai kuma akwai abubuwan da muke yi da su biyun amma ba da na farkon ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel