‘Yan Sanda sun kubutar da Jarirai da Masu juna biyu a Jihar Ribas

‘Yan Sanda sun kubutar da Jarirai da Masu juna biyu a Jihar Ribas

A tsakiyar makon nan mu ka ji cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, ta ce ta kubutar da jarirai 24 da Mata masu ciki hudu a wani gida jarirai da ke jihar Ribas.

Dakarun ‘Ya Sandan kasar sun yi wana bayani ne ta bakin Kwamishian ‘Yan Sanda na jihar Ribas, Mustapha Dandaura a babban birnin jihar Ribas na Fatakwal.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar The Cable, da ya ke bayani, ya bayyana cewa Jami’an tsaron sun kai samame a gidan jariran ne a Ranar Talata.

Kwamishinan ‘Yan Sandan ya ce an soma bincike domin a gano masu hannu wajen kafa wannan gidan jarirai inda Mata su ke haihuwan yaran da ake safararsu.

Kakakin ‘Yan Sandan Ribas, Nnamdi Omoni, shi ne ya wakilci Kwamishinan, har ya bayyana cewa akwai ‘Yan shekara guda cikin yaran da aka samu a gidan.

KU KARANTA: Iyalin Buba Galadima sun rabu bayan an karbe masa gida

“Dakarun Eagle Crack sun kai wani samame a jiya (Talata) da kimanin karge 3:00 na rana, su ka bankado wani gidan safarar jarirai da ke Woji, a Fatakwal.”

Jawabin Rundunar ‘Yan Sandan ya kara da cewa: “Jarirai 24 masu shekara daya zuwa biyu aka gano; an kuma ceto ‘Yan mata hudu masu dauke da juna biyu.”

Jariran da aka samu ‘yan shekara guda ne zuwa biyu, busassu masu fama da yunwa. Yanzu haka ana kula da su a wani babban asibiti da ke Garin na Fatakwal.

“Dakarun su na kira ga jama’a, musamman Mazauna jihar Ribas wadanda jariransu su ka bace, da su zo domin su gane su, su karbi yaransu.” Inji Kwamishinan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel