Tashin hankali: An kama ta saka saurayinta a cikin jaka ta datse da mukulli har sai da ya mutu

Tashin hankali: An kama ta saka saurayinta a cikin jaka ta datse da mukulli har sai da ya mutu

- Wata mata mai shekaru 42 ta shiga hannun ‘yan sanda a Florida a kan zarginta da akeyi da kisan saurayinta

- Matar ta sanar da cewa wasa suke bayan sun sha giya, shi kuwa da kan shi ya shiga akwati bayan nan ta bige da bacci

-Amma kuma bidiyon yadda lamarin ya faru ya saba don kuwa an ganshi yana bata hakuri tana ce mishi sakamakon cin amanarta da yake yi ne take ramawa

Wata mata mai shekaru 42 ‘yar asalin garin Florida mai suna Sarah Boone, ta shiga hannun jami’an tsaro a kan laifin kisan kai. An kama matar ne da laifin kashe saurayinta ta hanyar saka shi cikin akwati ta rufe na sa’o’i masu yawa.

Bayan kama matar, ta sanar da masu bincike cewa suna wasa ne da saurayinta mai suna Jorge Torrez Jr a ranar Litinin din, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya walllafa.

Tashin hankali: An kama ta saka saurayinta a cikin jaka ta datse da mukulli har sai da ya mutu
Tashin hankali: An kama ta saka saurayinta a cikin jaka ta datse da mukulli har sai da ya mutu
Asali: Facebook

Matar ta bayyana cewa a ranar 24 ga watan Fabrairu din sun sha giya ne sai suka fara wasan. Boone ta ce suna wasan ne sai Torrez ya shiga jakar mai launin bula a wajen gidanta da ke Orlando.

Wacce ake zargin ta ce ta kwanta bacci ne daga mayen giyar lokacin da ta hau bene shi kuwa Torrez yana cikin akwatin. Ta tashi daga baccin ne bayan da wayarta ta dinga kara sakamakon kiran da ya shigo.

KU KARANTA: Matashi ya kashe kanshi bayan tsangwamar da mutane ke yi masa, saboda ya zama dan luwadi

Ta jaddada cewa ta kira 911 bayan da ta tuna cewa saurayin nata yana cikin akwatin kuma yana kwance babu numfashi.

Amma kuma jami’an sun musanta abinda ta sanar don an ga bidiyonta da Torrez yana ihun neman dauki yayin da take azabtar da shi. An ga tana dariya yayin da take kiran sunansa kuma yana sanar mata cewa baya numfashi.

Rahoton kama Boone ya bayyana cewa, an ga tana sanar da shi cewa hakan ake ji yayin da aka daina numfashi. Sai yake sanar da ita numfashin shi na tafiya amma sai ta ce “Hakan ne zai faru da kai, ka dandana don haka nake ji nima idan ka ci amanata.” An ji ta tana ce wa Torrez ya rufe baki bayan rokonta da yake yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel