Saudiyya ta saka a cafko wata budurwa bakar fata da tayi waka taci mutuncin matan kasar

Saudiyya ta saka a cafko wata budurwa bakar fata da tayi waka taci mutuncin matan kasar

- Hukumomin kasar Saudi sun bukaci a damko wata mawakiyar gambara a kasar mai suna Ayasel

- Mawakiyar ta wake 'yan matan kasar ne tare da kwatanta kyan su da cewa tamkar alawa suke

- An cire wakar daga yanar gizo tare da toshe shafinta na YouTube inda kuma gwamnan Makka ya bukaci a damko ta don 'cin zarafin' matan da tayi

Jami'ai daga kasar Saudi sun bukaci kama wata mawakiyar gambara a kan wata bidiyon waka da ta saki cikin kwanakin nan. A bidiyon wakar mai suna 'Yan matan Makka', mawakiyar mai suna Ayasel Slay a kasar Saudi din ta saka riga iya kwaurinta tare da dankwali. Ta kwarzanta matan kasar Saudi din inda ta kirasu "masu rinjaye kuma kyawawa".

"Budurwar Makka ce kowa ke bukata, kada a bata mata rai don za ta rama," Ayasel ta ce a cikin wakarta da ke kwatanta cewa matan Makkan sun fi mata da yawa kyau da jarumtaka.

"Muna mutunta sauran 'yan mata amma matan Makka tamkar alawa ne," ta rera yayin da maza da mata ke rawa, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Saudiyya ta saka a cafko wata budurwa bakar fata da tayi waka taci mutuncin matan kasar
Saudiyya ta saka a cafko wata budurwa bakar fata da tayi waka taci mutuncin matan kasar
Asali: Facebook

Tuni dai aka rufe shafinta na YouTube kuma aka cire faifan bidiyon wakarta din bayan jami'an kasar sun yi ikirarin cewa ta yi batanci ga al'adun Makka kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Gwamnan Makka, Khalid al-Faisal ya bukaci a damko Ayasel tare da wadanda suka dau nauyin yin wannan wakar 'cin zarafin'.

Wakar kuwa ta jawo cece-kuce a yanar gizo, inda wasu ke kwarzanta gwamnatin da ta sauke wakar tare da bukatar a kama mawakiyar. Wasu kuwa sun kushe wannan lamarin.

"Wannan shirmen ya isa haka. Ina fatan za a hukunta wannan 'yar Afirkan kuma a mayar da ita kasarta." In ji wani a yanar gizo.

"Mayar da ita kasarta shine kawai. Dama bai dace ana ajiye kowanne bakin haure ba da suka zo daga kowanne yanki," wani mutum ya wallafa.

A yayin da wasu ke ganin hakan yayi dai-dai, wasu na ganin cewa basu yi dai-dai ba.

"Idan akwai abinda ya dace ku fatattaka shine yadda kuka dau banbancin launin fata." Wani ya wallafa a tuwita.

"Wannan halayyar gwamnatin Saudi ce. Suna kawo mawakan Turai amma kuma suna caccakar matan Saudi da suka fito don bayyana al'adunsu. A cikin wakar babu kalaman batanci ai," wani dan kasar Kenya yayi wa Gwamnan martanin abinda ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel