Wata sabuwa: Saudiyya ta bawa mata damar bude kungiyar kwallon kafa a kasar
- A kokarin da kasar Saudiyya take yi na ganin ta zamanantar da kasar ta kuma jawo hankalin mutanen duniya wajen shiga kasar yawon bude ido
- A wannan karon mun ci karo da wani labari da yake nuna cewa kasar ta bawa mata damar shiga a fafata da su a harkar wasannin kwallon kafa
- Kasar dai a shekarar 2018 ne ta cire dokar dake hana mata damar shiga filin kwallon kafa domin kallo
Hukumomin wasanni na kasar Saudiyya sun fitar da kungiyar kwallon kafa ta mata.
Duka dai wannan na zuwa ne a kokarin da Yariman kasar mai jiran gado, Mohammed bin Salman yake yi na ganin ya zamanantar da kasar a idon duniya.
Wasa na farko da za a fara yi na 'yan mata da suke sama da shekaru 17 a duniya, wanda za a bayar da kyautar ($133,000), za a gabatar da shi a biranen Jeddah, Riyadh da kuma Dammam, cewar hukumar wasanni ta kasar a jiya Talata.
Rahoton na AFP ya nakalto hukumar ta wasanni tana cewa "kaddamar da gasar zai kawo cigaba wajen mata a bangaren wasanni, kuma zai karawa matan kasar daraja a idon duniya ta fannin wasanni."
Wannan dai wani cigaba ne da matan kasar suka samu a bangaren wasanni, tun bayan cira dokar da take hana mata shiga filin buga wasan kwallon kafa da aka yi a kasar a watan Janairun shekarar 2018.
KU KARANTA: Tirkashi: Bazawara ta tonawa wani magidanci da ya nemi lalata da ita asiri
Kasar dai ta Saudiyya tana da tsohon tarihi wajen sanyawa mata tsauraran dokoki, wadanda suka hada da hana su harkoki a fannin wasanni kwata-kwata.
Sai dai a wannan lokacin kasar na kokarin karfafa fannin wasannin na mata a fadin kasar dama duniya baki daya.
Yariman kasar mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ya kawo sauye-sauye da yawa a kasar wadanda suka hada da wasanni da kuma mawaka na turawa suna shiga, bude wuraren silima, da kuma cire dokar hana mata tuki a fadin kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng