Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112

Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112

Wani tsohon dan asalin kasar Japan mai suna Chitetsu Watanabe wanda aka bayyana shi a matsayin mutumin da ya fi kowa yawan shekaru a duniya ya mutu yana dan shekara 112.

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1907 aka haifi Watanabe a kauyen Niigata dake Arewacin birnin Tokyo na kasar Japan, kuma ya mutu ne a ranar Lahadin da ta gabata a gidan kulawa da tsofaffi.

KU KARANTA: Yadda aka yi na zama sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna – Zailani

Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112
Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112
Asali: Facebook

Duka duka tsakanin samun kambun kasancewa wanda yafi kowa tsufa a duniya da rasuwarsa bai wuve makonni biyu na, kuma gidauniyar Guinness World Records ce ta bashi wannan kambu.

Dattijo Watanabe yana da yara biyar, kuma ya bayyana sirrin tsawon rai da ya yi ga “Kada ka sake ka yi fushi ko a bata maka rai, kuma kada yawaita murmushi.” Inji shi. Sai dai yace yana yawan shan askirim.

A yanzu haka mutumin da ya fi tsufa a Japan shi ne Issaku Tomoe dan shekara 110 kamar yadda kamfanin wallafa labarai ta Jiji ta tabbatar, sai dai babu tabbacin ko a duk duniya babu sa’ansa.

Haka zalika wanda ta fi tsufa a cikin mata ita ma yar kasar Japan ce, mai suna Kane Tanaka yar shekara 117. Alkalumma sun tabbatar da jama’an kasar Japan sun fi kowa tsawon rai a duniya, saboda yawaitan samun tsofaffin da suka dade a cikinsu.

Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112
Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, a wani labarin kuma, wata babbar kotun majistri dake zamanta a jahar Kano a karkashin jagorancin Alkali Aminu Gabari ta bayar da beli ga mutumin da ake tuhuma da kitsawa tare da watsa labarin auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocinsa Sadiya Umar Farouk da Zainab Shamsuna.

Ana thumar mutumin mai suna Kabiru Muhammad dan shekara 32 ne laifin kirkirar labarin karya game da auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministar kudi Zainab Ahmad da kuma ministar kula da yan gudun hijira, Sadiya Umar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng