Coronavirus: An haramta ci da sayar da kowanne irin nau'i na namun daji a kasar China

Coronavirus: An haramta ci da sayar da kowanne irin nau'i na namun daji a kasar China

- Gwamnatin kasar China a ranar Litinin ta zartar da dokar haramta kasuwanci da cin naman dabbobin daji

- Duk da gwamnatin kasar ba ta sauya dokokin bada kariya ga namomin dajin ba, ta zartar da sabuwar dokar ne saboda cutar covid-19

- Kamar yadda jaridar gwamnatin kasar ta bayyana, cutar ta kashe a kalla mutane 2,000 a duniya kuma ta kama mutane 79,700

Gwamnatin kasar China a ranar Litinin ta haramta ci ko kasuwancin naman dabbobin daji a matsayin hanyar kare kiwon lafiyar jama'a. Hakan ya biyo bayan danganta cutar Covid-19 da aka yi da cin naman dabbobin daji.

Hukumomin yada labarai a Xinhua sun ce an mika bukatar ne gaban NPC kuma tana bayyana haramcin cin naman da safarar shi kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Coronavirus: An haramta ci da sayar da kowanne irin nau'i na namun daji a kasar China
Coronavirus: An haramta ci da sayar da kowanne irin nau'i na namun daji a kasar China
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar gwamnatin kasar mai suna People's Daily ta bayyana, China ba ta sauya dokokin bada kariya ga namomin dajinta ba amma zartar da dokar da aka yi a ranar Litinin an yi ta ne da gaggawa saboda tsananin amfanin da take da shi. Dokar za ta yaki barkewar cutar da ta lashe rayuka 2,628 a duniya.

KU KARANTA: Babbar magana: Yadda na dinga sanya kanwata tana kwanciya da mijina - Matar aure

A fadin duniya, coronavirus ta kama mutane 79,700 kuma ta shafi a kalla kasashe 24 na duniya.

Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa cutar ta fara ne daga namun daji.

Gwamnatin kasar China din ta taba saka makamanciyar dokar nan a 2002 yayin da wata muguwar cuta ta barke wacce ta kashe daruruwan mutane a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel