Kwara
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kwara bayan wasu motoci guda biyu sun yi taho mu gama. Mutum 11 sun rasu yayin da wasu suka jikkata.
Wasu miyagun yan bindiga sun kai mummunan farmaki har cikin gidan wani babban likita a jihar Kwara. Yan bindigan sun halaka likitan tare da sace diyarsa.
Wata kotun majistire mai zama a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta garkame wani matashi da ya kashe mahaifinsa kan yana yi masa fada ba tare da aikata laifi ba.
Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara ya ziyarci jihar Kaduna don yin ta'aziyyar mutanen da suka mutu a harin bam tare da ba da tallafin Naira miliyan 200.
An samu tashin gobara har sau biyu a jihar Kwara. Gobarar wacce ta tashi daban-daban a rukunin shagunan ta kona shaguna guda 17 da lalata dukiyoyi.
Gwamnatin jihar Kwara ta ce babu wani dalili da zai saka a sayar da babban otel din jihar, kawai ta yi gwanjon kayan cikinsa ne don yin gyare-gyare.
Mai martaba Sarkin Ilorin ya ce tun da aka kafa hukumar EFCC bai taɓa zuwa ya nemi a taimaka a kyale wani da hukumar ke tuhuma da aikata wasu laifuka ba
Babbar kotun da ke jihar Kwara ta daure Sarkin Fulanin Kwara, Usman Ado da wasu mutane biyu kan zargin garkuwa, ana zargin sun yi garkuwan ne da wani soja.
Allah ya yi wa tsoffin yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kwara rasuwa. Yan majalisar biyu sun mutu ne cikin awanni 48 a tsakani. Gwamnan jihar ya yi martani.
Kwara
Samu kari