IGP Ga Jami'an Yan Sanda: Aikin Ku Zai Iya Jefa Ku Wuta Ko Aljanna Ranar Gobe Ƙiyama

IGP Ga Jami'an Yan Sanda: Aikin Ku Zai Iya Jefa Ku Wuta Ko Aljanna Ranar Gobe Ƙiyama

  • Sufetan yan sanda, Usman Alkali Baba, ya yabawa jami'an yan sanda dake aiki a jihar Kwara bisa namijin kokarin da suke wajen tabbatar da tsaro
  • IGP ya shaidawa jami'an cewa wannan aikin da suke na al'umma ne, zai iya jefa su cikin aljanna ko wuta ranar kiyama
  • A cewarsa, ya zama wajibi akan kowane jami'i ya yi iyakar kokarinsa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa na tabbatar da doka

Abuja - sufeta janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, IGP Usman Baba, ya yabawa jami'ansa da sauran hukumomin tsaro bisa namijin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro a jihar Kwara, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Da yake jawabi ga jami'an rundunar yan sanda, yayin ziyarar da yakai Ilorin ranar Laraba, Baba ya bukaci jami'an su sadaukar da kansu ga aikinsu kuma su guji duk wani abu da ka iya ɓatawa rundunar yan sanda suna.

Kara karanta wannan

Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna

IGP Usman Alkali Baba
IGP Ga Jami'an Yan Sanda: Aikin Ku Zai Iya Jefa Ku Wuta Ko Aljanna Ranar Gobe Ƙiyama Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

IGP Baba yace:

"Kun zo nan ne domin gudanar da aikin tabbatar da doka, mafi yawancin ku daga wasu sassan Najeriya kuka fito. Rundunar yan sandan ƙasa ne ku ba wai na jihar Kwara ba."
"Saboda haka ya zama wajibi mu maida hankali kan aikin mu, sannan ina son taya ku murna domin jihar Kwara ta fi ko ina zaman lafiya idan aka kwatanta da sauran jihohi."

Kakin ku zai iya sa ku shiga Wuta ko Aljanna

Bugu da kari, sufetan yan sanda ya bayyana wa jami'ansa cewa wannan aikin da suke yi zai iya jefa su Wuta ko Aljanna a ranar gobe kiyama, ya danganta da yadda suka sauke nauyin dake kansu.

Vanguard ta ruwaito IGP na cewa:

"Idan kuka sadaukar da kanku a matsayin jami'an tabbatar da doka, to kuna da sakamako ba anan duniya ba kaɗai, har ranar Lahira saboda aikin ku na al'umma ne."

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

"Wannan kakin da kuka saka zai iya sa ku shiga Aljanna kuma zai iya jefa ku Wuta. Ya danganta da yanda kuka ci ɗamarar gudanar aiki da shi."

A wani labarin kuma Ba Zan Bada Hakuri Ba Kan Kalaman da Na Yiwa Shugaba Buhari, Gwamna Ebonyi

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, yace sam babu bukatar ya bada hakuri kan kalaman da ya yiwa shugaba Buhari.

Gwamnan ya kuma bayyana jin daɗinsa bisa ziyarar Ali Modu Sherif, wanda ke neman tikitin zama shugaban APC na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel