Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari

Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari

Matsaloli sun yi yawa a tsakanin gwamnonin Najeriya na yanzu waɗanda ke ƙoƙarin kawo ƙarshen su da kuma ganin sun isar da ribar dimokraɗiyya kamar yadda aka bayyana a cikin alkawuran kamfen ɗinsu kafin su hau kan mulki.

An yi amfani da muhimman sigogi kamar tsaro, ilimi, samar da dukiya, ayyukan yi, cibiyar lafiya, da ci gaban ababen more rayuwa wajen kimanta gwamnonin jihohi akan kokarinsu.

A waɗannan bangarori na shugabanci, wasu gwamnoni a faɗin ƙasar sun yi abin da ya cancanci a ambace su tare da yaba masu.

Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari
Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari Hoto: Vanguard, Guardian
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro jerin gwamnoni 5 wadanda babu kasa a gwiwa ba wajen ganin mafarkin al’ummansu ya zama gaskiya.

1. Gwamna Babajide Sanwo-Olu (Lagos)

Gwamnan Legas wanda ya hau kujerar mulki a 2015 a karkashin jam’iyyar All progressives Congress (APC) ya yi iyakacin kokarinsa don ganin ya hada kan tsohuwar babbar birnin kasar tare da yin aiki mai kyau ga mutanen Legas.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

Kan lamarin tsaro, duba ga yadda ya tafiyar da al’amarin zanga-zangar EndSARS da abin da ya biyo baya, Sanwo-Olu ya tabbatar da cewa shi jagora ne wanda a halin yanzu yake sanya soyayyarsa a zukatan jama'arsa.

Wannan baya ga rawar da gwamnatin jihar ke takawa wajen tallafawa kamfanoni masu zaman kansu (daga cikin dalilin da ya sa ya sami takardar shaidar Guiness World Record) da tsarin sufuri a daya daga cikin manyan biranen Afirka.

2. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara)

Ko shakka babu gwamnatin Gwamna AbdulRazaq ta sauya jihar zuwa matakin nasara bayan da ta sami ci gaba mai yawa don amfanin jama'a.

Duk da cewa AbdulRazaq ya tsara wa Kwara sabon kwas ta kowane fanni, amma da gangan ya gudanar da gwamnati mara nauyi ta amfani da taimakon majalisar ministoci, matakin da ke da fa'ida sosai ga tattalin arzikin Kwara.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Dangane da waɗannan da ƙari, gwamnan a ranar Alhamis, 9 ga Satumba ya karɓi lambar yabo ta gwarzon jaridar Jaridar Leadership.

3. Gwamna Nyesom Wike (Ribas)

Mutum mai ra’ayin mazan jiya a cikin jihar mai arzikin mai ba a banza ake masa laƙabi da Sarkin aiki ba. Manyan nasarorin da Gwamna Wike ya samu a jihar ya sa mutanensa basa gajiya da yabonsa.

Ba tare da niyyar ci gaba da zama a mulki na wani wa’adi ba, Wike ya fara aiwatar da aiki daya bayan daya a cikin sauri.

Dangane da wannan, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya yarda cewa gwamnan mai son jama'a ya cancanci sunan.

4. Gwamna Ifeanyi Okowa (Delta)

An san Okowa a matsayin daya daga cikin gwamnonin Najeriya na farko da suka amince da cin gashin kan bangaren doka da na shari’a a daidai lokacin da fafutukar samun madafan iko tsakanin bangarorin gwamnati ya yi yawa.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

Haka kuma, kamar Wike, gwamnan na Delta ya kuma yi wa jama'arsa abubuwa da yawa ta fuskar ababen more rayuwa, tsaro da sufuri.

5. Gwamna Babagana Zulum (Borno)

Idan akwai gwamna ɗaya a cikin ƙasar wanda da kansa yake sa ido kan yadda ake amfani da kuɗin jihar, shine Gwamna Zulum.

Gwamnan na Borno yana tafiye-tafiye na kashin kansa don duba cibiyoyin jihar (kiwon lafiya, ilimi da tsaro) don ganewa idanunsa yadda ake kula da su.

Har ila yau, an san Farfesan a matsayin daya daga cikin gwamnonin da ma'aikata basa bi albashin ko sisi amma duk da haka baya kallon wannan a matsayin nasara.

Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan APC ya ba takarar Asiwaju Bola Tinubu gagarumar goyon-baya gadan-gadan

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Zulum ya kasance dalibin kwalejin kimiyyar daga shekarar 1986 zuwa 1988.

Ya sami difloma a bangaren Injinyan Noma kafin ya koma makarantar a matsayin shugaba daga 2011 zuwa 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel