'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Dagajin Ƙauyen Bororo Sun Kashe Shi a Kwara

'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Dagajin Ƙauyen Bororo Sun Kashe Shi a Kwara

  • 'Yan bindiga sun halaka Alhaji Sheidu Madawaki, jagoran garin Bororo a karamar hukumar Irepdun jihar Kwara
  • Majiya daga iyalan mamacin ya bayyana cewa yan bindigan su uku ne suka kutsa gidansa suka bindige shi
  • Wata majiyar tsaro ta ce iyalan mamacin na zargin an kashe shi ne saboda kusancinsa da jami'an tsaro

Jihar Kwara - Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun halaka, shugaban garin Bororo a Oro-Ago, karamar hukumar Irepdun, jihar Kwara, Alhaji Sheidu Madawaki, a daren ranar Lahadi, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Wata majiya daga iyalansa, da suka yi magana da Daily Trust sun ce maza uku dauke da bindigu ne suka kutsa gidan jagoran na garin Bororo misalin karfe 9.30 na daren Lahadi suka bindige shi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu matan aure a Zariya

'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Dagajin Ƙauyen Bororo Sun Kashe Shi a Kwara
Taswirar Jihar Kwara: Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta kara da cewa:

"Su uku ne. Daya daga cikinsu ya tsaya a wajen gidan yana ta harbe-harbe yayin da biyun suka shiga gidan suka bindige shi a uwar dakansa.
"Sun zo ne dauke da bindigu da ake zargin AK-47 ne hakan ya janyo firgici da tsoro a garin."

An tattaro cewa jami'an tsaro da suka hada da yan sanda da jami'an tsaro na NSCDC reshen Oro Ago sun ziyarci wurin da abin ya faru a ranar Litinin.

Wata majiya ta ce marigayin ya ziyarci ofishin NSCDC makonni biyu da suka gabata a ranar Litinin, "domin hadin gwiwa da jami'an tsaron kan yadda za a inganta zaman lafiya a masarautar.
"Ya jadada bukatar da ke da akwai na kare masu bawa jami'an tsaro jami'an tsaro kuma aka tabbatar masa."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Wani majiya na tsaro ya ce hakan ya sanya wasu daga cikin iyalansa zargin cewa yan bindigan sun halaka shi ne kada ya tona musu asiri.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin NSCDC na jihar Kwara amma hakan ya ci tura.

Majiyar tsaro ta tabbatar da afkuwar lamarin

Amma, wata majiyar tsaro ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa:

"An fara bincike a kan dalilin kai harin."

Majiyar ta kara da cewa:

"Amma yanzu, muna zargin akwai yiwuwar an kashe shi saboda kusancinsa da jami'an tsaro da niyyarsa bawa jami'an tsaron goyon baya."

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

A wani labarin daban, Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
Online view pixel