Yadda wani mutum ya dirka wa direban keke-napep duka nan take ya mutu

Yadda wani mutum ya dirka wa direban keke-napep duka nan take ya mutu

  • Rundunar 'yan sanda sun cafke wani mutum da laifin kashe direban keke-napep a jihar Kwara
  • Kisan nasa ya biyo bayan cacar baki da suka yi bayan da mai keke-napep din ya bugi wata mota
  • A hain yanzu ana ci gaba da bincike, kuma an sanar da cewa za a gurfanar dashi a gaban kotu

Kwara - An zargi wani direban keke-napep mai suna Kola Adeyemi da laifin dukan wani dan uwansa mai keke-napep a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Daily Trust ta tattaro cewa wanda ake zargin, Kayode Oluwatomi, wanda aka fi sani da “lawyer” ma’aikaci ne na kamfanin tuntuba na BYC da ke yankin Irewolede a Ilorin.

An ce ya farma mamacin ne saboda ya bugi abin hawansa ta baya.

Kara karanta wannan

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

Tribune Nigeria ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin 14 ga watan Satumba da misalin karfe 4:30 na yamma.

Yadda wani mutum ya lakadawa wani direban keke-napep duka har ya mutu
Taswirar jihar Kwara | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wani da abin ya faru a kan idonsa, lamarin ya fara ne a cikin zafafan musayar kalmomi tsakanin mutanen biyun.

A cewar shaidan gani da ido:

“Mutumin cikin fushi sai ya bugi mai keke-napep din da wani abu da ake zargin laya ne sai mutumin ya fadi ya mutu nan take.
"An ajiye gawarsa a Asibitin Garin Alimi, Asa Dam kuma 'yan sanda sun shiga lamarin."

'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) na jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce mataimakin shugaban kungiyar masu tuka keke-napep, rukunin Garin Alimi/Asa-Dam, Ilorin ne ya kawo rahoton karar gaban hukumar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

A cewar Okasanmi:

“Laifin kisan kai ne kuma mamacin na yankin Boluwaji, Egbejila, ya bugi wata mota kirar Honda mai launin baki tare da lamba Bx 954 AJL a baya kuma ya fasa daya daga cikin fitilun motar da darajarsu ta kai N2,500."

Okasanmi ya kara da cewa:

“Mai keke-napep din ya roki ya biya N2,000 amma shi (Kayode) ya ki sai rigima ta biyo baya wanda hakan ya sa ya mari mai keke-napep din nan da nan ya fadi sannan aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin Garin Alimi, Ilorin."

Ya ce wanda ake tuhuma, wanda tuni aka kama, za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

A wani labarin, Mutane uku sun mutu a Majalisar Karamar Hukumar Abuja (AMAC) ranar Lahadi 12 ga watan Satumba bayan ambaliyar ruwa.

Ambaliyar, sakamakon ruwan sama, ya sa motoci sun nutse, inda kadarori da dama suka lalace.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Akinfolanre Olowofele, mazaunin Trademore Estate a yankin Lugbe na AMAC, ya bayyana lamarin a matsayin "babban rashi".

Ya ce kimanin mutane bakwai aka ruwaito sun mutu a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel