Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

  • Prince Samuel Adedoyin, wani hamshakin dan kasuwa ne dan asalin jihar Kwara, ya rasa diyarsa, Princess Lola Olabayo ranar Talata
  • Mummunan lamarin ya faru ne bayan wata biyu da Subomi, dan sa ya halaka kansa, duk da dai ba a san kwakkwaran dalilinsa na yin hakan ba
  • Rahotanni sun tabbatar da yadda ta kwashe kwana bakwai a asibitin jihar Legas tana fama da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19

Kwara - Prince Samuel Adedoyin, wani hamshakin biloniya dan asalin jihar Kwara ya rasa diyarsa, Princess Lola Olabayo.

Mummunan lamarin ya faru ne yana tsaka da jimamin mutuwar dansa Subomi da watanni biyu bayan ya yi ajalin kansa, duk da dai ba asan dalilinsa nayin hakan ba.

An samu labarin yadda ta rasu a asibitin jihar Legas bayan kwashe kwana 7 kwance sakamakon fama da cutar COVID-19.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya yi shekara 41 yana shari’a da makarantarsa ya mutu bayan ya ci nasara

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa
Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai wata majiya daga iyalinsa wacce bata bukaci a bayyana sunanta ba, ta musanta cewa cutar ce ta kashe ta.

Mahaifin mamaciyar ya tabbatar da mutuwarta inda yace za su sanar da ranar da za a yi bikin birneta.

A cewarsa:

Ta rasu a ranar Talata da daddare a asibitin Legas. Za mu yi taron mu na ‘yan uwa don tattaunawa akan ranar da za a tsayar don a yi bikin birne ta. Za mu saki takarda bayan mun kammala taron, a cewar mahaifin mamaciyar.

Bayan wakilin Daily Trust ya kai ziyarta gidan Olobayo dake GRA a ranar Laraba, ya taras babu mutane sosai.

Funke, daya ce daga yaran Adedoyin kuma ta rasu ne a 2018.

Ta rasu ne lokacin tana rike da kujerar ‘yar majalisar wakilai bayan tayi fama da cutar daji.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Da kaca aka daure Igboho a Cotonou don gudun kada ya zama Mage ya tsere, Lauyansa

Daya daga cikin lauyoyin mai assasa samar da kasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya bayyana yadda ‘yan sandan jamhuriyar Benin suka daddaure Igboho da kaca don gudun kada ya rikida ya koma mage kuma ya tsere daga hannunsu a filin jirgin kasar.

Kamar yadda saharareporters suka ruwaito, Olusegun Falola ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa Igboho ziyara a inda aka tsare shi.

A cewar Falola, jami’an ‘yan sandan sun ji tsoron ya bace a cikin iska saboda bakin tsafinsa mai cike da al’ajabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: