‘Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sake kai hari, sun kashe makiyayi watanni bayan kisan ɗan'uwansa
- An jefa iyalan wani makiyayi a jihar Kwara cikin jimami sakamakon mutuwar wani Ibrahim
- 'Yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun kutsa cikin harabar gidan makiyayin sannan suka garkame shi har ya mutu
- A cewar rahoton, dan uwan wanda abin ya rutsa da shi shima ya rasa ransa a farkon shekarar 2021, a wannan gida
Kwara - Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sake kai hari Kwara, a wannan karon, sun kashe wani makiyayi.
An garkame makiyayin da aka bayyana sunansa da Ibrahim har lahira yayin harin da aka kai a ranar Alhamis, 30 ga watan Satumba.
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC a Kwara, Babawale Afolabi ya saki wata sanarwa inda yake tabbatar da mummunan lamarin.
Afolabi ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kai farmaki harabar gidan makiyayin sannan suka bar shi cikin jininsa, TheCable ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“An kawo rahoton marigayin zuwa ofishinmu a ranar Juma’a, ta hannun jami’inmu na Oro Ago, Najimu Lawal.
"Wannan Bafulatani makiyayin, wanda aka fi sani da Ibrahim ko lbro, maharan sun kai masa farmaki sannan suka garkame shi har lahira."
An fara farautar maharan
An kaddamar da farautar wadanda suka aikata wannan aika-aika wadanda har yanzu suna da yawa. Idan aka kama su, za a gurfanar da su bayan bincike, a cewar kakakin, Premium Times ta rahoto.
Afolabi ya kara bayyana cewa dan uwan mamacin ya rasa ransa a farkon shekarar 2021, a wannan gidan da ka kashe marigayin.
Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja
A wani labari na daban, mun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari da aka kai garin Kagara da fadar Sarkin, a jihar Neja.
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Minna, babbar birnin jihar, jim kadan bayan ya ziyarci sojoji goma sha biyu da suka jikkata wadanda ke karbar magani a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida.
Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin sojojin da suka jikkata suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke Kaduna, sashin Hausa na BBC ya kuma ruwaito.
Asali: Legit.ng