Hoton Mutumin Da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Gidan Yari Bayan An Kama Shi Yana Satar Doya
- Wata kotun majistare a jihar Kwara ta yanke wa wani Abubakar Buni daurin watanni shida a gidan yari
- Alkalin kotun ya yanke wa Buni hukuncin ne bayan ya amsa tuhumarsa da ake yi na satar doya daga gonar wasu
- Jami'ian hukumar NSCDC na jihar ne suka gurfanar da shi a kotu bayan wani makwabcinsa ya yi korafi a kansa
Jihar Kwara - Wata kotun majistare na Jihar Kwara da ke zamanta a Kaiama ta yanke wa wani Abubakar Bani, dan shekaru 28 hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda satar doya.
Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Kwara ne ta gurfanar da Bani saboda satar doya a kauyen Tenebo, a karamar hukumar Kaiama da ke jihar, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A rahoton LIB, Mai magana da yawun hukumar a jihar, Babawale Afolabi, ya ce wani Ismaila Ebbo Mohammed da makwabtansa da Kibefandi ne suka kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Agustan 2021, misalin karfe 6 na safe.
Ya ce:
"A cewar wadanda suka kai korafin, bafulatanin ya dade yana zuwa satar doya a gonar a kowanne rana. Wanda ake zargin, Abubakar, ya amsa cewa ya aikata laifin kuma nan take kwamandan NSCDC na jihar Kwara, C.C. Makinde Iskil Ayinla, ya bada umurnin a gurfanar da shi a kotu."
Jami'in hulda da jama'an ya kara da cewa:
"An gurfanar da Abubakar Bani a kotun Majistareda ke Kaiama nan take, tunda wanda ake zargin ya amsa laifinsa. Don haka Alkalin Kotun, Yusuf Kide, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali na New Bussa jihar Niger bisa laifin kutse da sata."
Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa
A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.
Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.
Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng