An dakatar shugaban wata makarantar Larabci da aka ci zarafin wata daliba
- An samu wani bidoyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka ga ana dukan wata daliba
- Gwamnatin jihar Kwara ta ce ba za ta yi shuru kan batun ba, inda tace za a dauki matakin a tsanake
- A halin yanzu an dakatar da shugaban makarantar har zuwa lokacin kammala bincike kan lamarin
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta fara gudanar da bincike kan cin zarafin wata daliba a makarantar Larabci da malamai suka yi.
Gwamnati ta kafa kwamitin bincike, wanda ya kunshi malaman Muslunci, shugabanni da jami’an gwamnati, domin duba lamarin yayin da aka dakatar da shugaban makarantar har sai an kammala bincike.
Sanarwar da Kwamishinan Ilimi da Ci Gaban Bil Adama, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa gwamnati ta kuma kai daliban da abin ya shafa zuwa asibitin gwamnati don duba lafiyarsu da kuma kula da su.
Sanarwar ta ce:
“Wakilan Gwamnatin Kwara sun ziyarci makarantar Larabci wacce aka ga dalibanta a wani faifan bidiyo ana azabtar da su saboda saba wa dokokin makarantar.
Kwamitin da ke bincike kan lamarin
Legit.ng Hausa ta tattaro daga cikin sanarwar, inda ta bayyana jami'an da ke cikin tawagar kamar haka:
- Hon. Kwamishinar ilimi da bunkasa jarin dan Adam, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu
- Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Addini (Musulunci) Alhaji Danmaigoro
- Dr Saudat AbduBaqi na Jami'ar Ilorin
- Mallam Lawal Olohungbebe na Jami'ar Jihar Kwara
- Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Rafiu Ajakaye
- jami’in 'yan sanda na yankin Ganmo SP Oko Nkama
- Wakilin NSCDC, DSC Parati AbdulHameed.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa:
“Tawagar gwamnati a tsanake ta saurari mahukuntan makarantar Larabcin, mahaifin yarinyar da aka gani a bidiyon, da wasu dalibai hudu da ke da hannu cikin batun mara dadi.
"Duk bayanin da hukumomi suka bayar kan lamarin, yardar da iyaye suka yi da kuma nadamar daliban da abin ya shafa, gwamnati ta nuna bacin ranta sosai kan mummunan duka da aka gani a bidiyon.
Gwamnati ta mayar da yara 360,000 da basa zuwa makaranta zuwa ajujuwa a Katsina
A wani labarin, Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Gwamnatin Katsina ta ce sama da yara 360,000 ne a jihar suka yi rajista a makarantu tun daga shekarar 2019.
Abdulmalik Bello, daraktan wayar da kan jama’a, Hukumar Ilimi ta bai-daya ta jihar Katsina (SUBEB) ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba.
Ya bayyana haka ne a wani taro da ‘yan jarida kan shirin komawa makaranta da kuma yakin neman canji da aka kaddamar a jihar.
Asali: Legit.ng