EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

  • Jami'an Hukumar EFCC sun kai samame jami'ar Jihar Kwara wato KWASU
  • Sun yi nasarar kama kimamin dalibai 30 da ake zargi 'yan damafar intanet ne
  • Jami'ar ta ce daliban ba a makaranta suka koya ba, dama daga gida soka koya

Ilorin - Jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFFC reshen Ilorin sun kama wasu dalibai 30 da ake zargi 'yan damfara ta intanet ne a Jami'ar Jihar Kwara wato KWASU da ke Malete, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar ta ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayannan sirri game da su na aikata damfara da yaudara ta yanar gizo wato intanet.

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU
Jami'an Hukuma EFCC. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shugaban sashin hulda da jama'a na EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana hakan cikin wat sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya kara da cewa sun shafe makonni biyu suna saka ido a kan wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

A cewarsa, cikin bayannan sirrin da suka samu ya nuna cewa wadanda ake zargin suna damfarar ne daga dakunansu na makaranta suna damfara mutanen Ilori da kewaye.

Ya ce:

"Bisa bayannan sirri da makonni da muka dauka muna sa ido a kansu, jami'an hukumar mu a ranar 19 ga watan Satumban 2021, sun samu izinin bincika dakin dalibai a KWASU inda aka kama wasu.
"A yayin tambayiyi, an saki wadanda aka gano ba su da hannn an mika su ga kungiyar shugabannin dalibai, SUG, na makarantar, yayin da wadanda ake zargin kuma an tafi da su Ilorin domin zurfafa bincike."

Ya kara da cewa abubuwan da aka kwato a hannunsu sun hada da motoccin alfarma shida, kwamfuta laptop da dama, wayoyin salula da wasu abubuwan zargi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Ya ce za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.

Ba a KWASU suka zama haka ba

Da ya ke martani kan lamarin, direktan watsa labarai na KWASU, Razaq Sanni ya shaidawa Daily Trust cewa wadanda aka kama din dama sun saba da mummunan halinsu tun kafin su zo makarantar.

Ya ce:

"Ba a KWASU suka koya wannan ba dama daga gida suka koyo. Wadanda aka kama din a dakin dalibai na wajen makaranta suke.
"Munyi imanin cewa da wannna tare da wayar da kai da muke yi da shugabannin SUG, za a rage matsalar sosai idan ma ba a kawar da ita baki daya ba."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel